Almajirai da ƴan jari-bola mazauna babban birnin tarayya Abuja da suka hada har da kananan ƴan kasuwa, da sauransu, sun shigar da kara akan ministan Abuja, Nyesom Wike, inda su ka bukaci ya biya su diyyar Naira miliyan 500 bisa zargin sa da tauye ƴancin su na yan ƙasa.

Kotun Daukaka Kara ta kama Trump da laifin Cin Zarafin Yarjarida

Wani lauya mai suna Abba Hikima ne ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1749/3024 a gaban mai shari’a James Omotosho na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a madadin rukunin mutanen.

Hikima, wanda aka ambata a matsayin mai shigar da ƙara a cikin takardar ƙarar da aka fitar a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2024, amma aka shigar a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2024, ya ce ya kai kara ne domin al’umma domin kare ƴan kasa masu rauni a Najeriya.

Kotu Ta Kori Karar Da Aka Shigar Akan Shugaban Kantin Kwari Balarabe Tatari

Masu ƙarar, kamar yadda Daily Trust ta rawaito, na ya haɗa da Wike, Sufeto-Janar (IG) na ‘yan sanda; Darakta-Janar, Sashen Sabis na Jiha (DSS) da Hukumar Tsaron farar hula (NSCDC) a matsayin waɗanda ake kara na 1 zuwa 4.

Lauyan ya kuma hada da Babban Lauyan Tarayya (AGF) da Gwamnatin Tarayyar Najeriya a matsayin waɗanda ake kara na 5 zuwa 6.

Kotun Koli ta kori Bukatar Sauke Tinubu Daga Mulki Akan Zargin Ta’ammuli Da Kwaya

Ya kuma nemi a biya Naira miliyan 500 a matsayin diyya saboda take hakkin ƴan kasa da abin ya shafa.

Nigerians Would Enjoy Free Rides on Abuja Metro Train-Tinubu

Ya yi roko ga kotun da ta bayyana cewa “kame ba bisa ka’ida ba, tsarewa ba tare da tuhuma ba, cin zarafi da karbar kuɗaɗe a wajen wadanda ba su da matsuguni, ‘yan banga, kananan ‘yan kasuwa, mabarata da sauran ‘yan Najeriya marasa galihu mazauna babban birnin tarayya Abuja, ya zama cin zarafi da take ƴancin su na yan kasa

Biz Point

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version