Gwamnatin Tarayya ta yi maraba da karin kima da kamfanin Moody’s Investors Service ya yi wa matsayin bashi na dogon lokaci na Najeriya daga Caa1 zuwa B3 tare da yanayin dindindin (Stable Outlook).
Wannan na nuna amincewar kasashen duniya kan sabon tsarin tattalin arziki da shirye-shiryen gyara da gwamnati ke aiwatarwa.
Kano Government Appoints Bashir Muzakkari SA Digital Economy
Wannan karin kima na nuna karuwar fahimtar duniya game da ci gaban Najeriya wajen daidaita tattalin arziki, kara gaskiya a harkokin kudi, kyautata tsarin basussuka, da aiwatar da gyare-gyaren kasuwa a karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cewar kamfanin Moody’s, wannan ci gaba ya samo asali ne daga “ingantaccen matsayi na kudin gwamnati, karfafa kasuwannin waje, da kuma jajircewar gwamnatin Najeriya wajen aiwatar da manufofin tattalin arziki da gyare-gyare.
Pilgrims Praise Kano Govt’s Accommodation in Madina
” Wannan ya hada da matakan da aka dauka na hade kasuwar musayar kudade, cire tallafin man fetur, kara samun kudaden shiga daga fannin da ba mai ba, da kuma dawo da kwarin gwiwa ga manufofin kudi ta hanyar aikin babban bankin Najeriya.
Yayin da yake mayar da martani game da wannan cigaba, Shugaba Tinubu ya jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da gudanar da tattalin arziki cikin tsari da kuma tabbatar da ci gaban da ya shafi kowa da kowa.
“Wannan karin kima na nuna wa masu zuba jari da abokan hulda na duniya cewa Najeriya ta dawo kan hanyar gyara, tsari da mutunci. Ya nuna jajircewarmu wajen gaskiya, da’a, da walwalar dukkan ‘yan Najeriya,” in ji Shugaba Tinubu.
Wannan karin matsayi zai taimaka wajen samun saukin shiga kasuwannin kudi na duniya, rage kudin bashin kasa, da jawo masu zuba jari daga kasashen waje, wanda zai kara habaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da gyare-gyare tare da karfafa juriyar tattalin arzikin Najeriya. Za a ci gaba da fadada hanyar samun haraji, zurfafa tattalin arzikin zamani, habaka masana’antu, da tallafawa masu rauni ta hanyar shirye-shiryen tallafin jin kai.
“Wannan karin kima ya kara tabbatar da kwarin gwiwar kasashen duniya ga makomar Najeriya kuma yana nuna matakin tarihi wajen dawo da amincewar masu zuba jari, habaka tattalin arziki, da tabbatar da dorewar ci gaba,” in ji Shugaba Tinubu.