Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), reshen Kano/Jigawa, ta kama kudaden waje da darajarsu ta haura naira miliyan 650 a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano (MAKIA).
Shugaban ofishin NCS Dalhatu Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin mika kudaden da wanda ake zargin ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a hedikwatar Kwastam da ke Kano.
NCS Intercepts N650M in Undeclared Foreign Currency at Kano Airport
Ya bayyana cewa kudaden an kama su ne daga hannun wani dan kasar Ghana, Ahmad Salisu, wanda ya iso daga kasar Saudiyya ta jirgin Ethiopian Airlines a ranar 7 ga Yuli, 2025.
Ya ce an cafke shi bayan ya kasa bayyana adadin kudaden da ke hannunsa kamar yadda doka ta tanada.
“Binciken da aka yi cikin kayansa ya gano dalar Amurka $420,900, faranshin CFA na Yammacin Afirka XOF 3,946,500, faranshin CFA na Tsakiyar Afirka XAF 224,000, da kuma fam na Ingila £5,825,” in ji Kwamfutalan Abubakar. “Jimillar darajar kudaden ta kai ₦650,987,268.50.”
Ya kara da cewa hadin gwiwar da aka samu tsakanin hukumar Kwastam da EFCC ne ya ba da damar nasarar wannan kama.
NCS Intercepts N650M in Undeclared Foreign Currency at Kano Airport
EFCC Ta Yaba Da Ayyukan Kwastam, Ta Tunatar Da Muhimmancin Bin Doka
A yayin karbar kudaden da wanda ake zargin.