Jagorancin Northern Youth Forum (NYF) na mika godiya da jinjina ga Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman Sale, da tawagarsa bisa nasarar gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin kwarewa da nagarta.
Shugabancinku ya samar da manyan nasarori da suka yi daidai da Shirin Renewed Hope Agenda Na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman ta fuskar yin komai a bayyane, rage farashi a sassa daban-daban, samar da VIP Tent A ga Alhazai, da kuma tallafin Shugaban kasa ga aikin Hajjin 2024.
NAHCON Ta Shirya Taron Masu Ruwan Da Tsarki Akan Hajjin Bana
Haka kuma abin a yaba ne, yadda Shugaban Kasa ya sahale Naira biliyan 90 domin rage karin kudi ga Alhazai, dakuma Naira biliyan 24 domin biyan bashin kamfanonin jiragen sama na 2023, tare da taimakon gwamnati wajen shawo kan masu jigilar Alhazai su karɓi kudin gida maimakon dalar Amurka, wanda hakan ya kare Alhazai daga fargabar karin tashin farashin canjin kudi.
EFCC Detains NAHCON Chairman’s Brother Over Alleged ₦50bn Hajj Fraud
Wadannan matakai sun sauƙaƙa wa Alhazai nauyi tare da ƙara tabbatar da amana da kwarin gwiwa a kan NAHCON. Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da taimakonku wajen hidima ga al’ummar Musulmi da kuma ƙasarmu baki ɗaya.
Comrade Yahaya Usman Kabo
Chairman, NYF