Shugaban kungiyar ‘yan Kasuwar Kantin Kwari Alhaji Balarabe Tatari ya ce Sun samar da matasa sama da guda dari bakwai da zasu samar da tsaro a lunguna da sakunan Kasuwar yayin zanga zangar lumana.

Alhaji Balarabe ya bayyana hakan ne Jim kadan bayan wani zagaye tare da wani rukuni na matasan domin tabbatar da lafiya da dukiyoyin ‘yan Kasuwar.

A cewar shi sun yi zama na tattuanawa tare da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci dake fadin jihar Kano domin lalubo mafita akan Kare dukiyoyin su.

Ya ce a baya sun ga yadda batagari ke shiga cikin masu zanga zangar lumana domin fasa shaguna da wuraren kasuwanci domin diban kaya saboda son zuciya.

Shugaban ya ce sun zabo masu bayar da tsaron ne daga kungiyoyi daban daban tare da samar musu riguna da katin shaida bayan an tntance su.

Read Also : Hunger protest: Kano Business Community constitutes committee to ensure security

Balarabe ya kara da cewar sun raba matasan a muhimman gurare daban daban dake fadin Kasuwar saboda gudun batagari su lalata kayan da ba nasu ba.

Ya Kuma yi kira ga matasan da su jajirce wajen sauke nauyin daya rataya a wuyan su,domin a cewar shi kasuwar ta Kwari na cikin manyan kasuwanni da ake jinda su a fadun nahiyar Afirka da ma Nigeria baki daya.

“Kasuwar ta yi shura wajen samar da ayyukan yi ga matasa tsawon shekaru da dama haka zalika akwai Anguwannin da suke jikin Kasuwar Wanda duk wani abunda ya shafe ta ya shafe su”

Read More: Kwari market association elects new executive

Shugaban Kasuwar ta Kantin Kwari ya kuma yi kira ga masu zanga zangar da su gudanar da harkokin su cikin lumana tare da gujewa sabawa dokar domin cigaban jihar Kano.

Balarabe Tatari ya Jajantawa dukannin wadanda iftilain fasa shaguna ko rauni ya afkawa tare da adduar Allah ya Kare na gaba.

Read Also: Kano Traders Seek Cut In Taxes, Other Charges

Idan zaku iya tunawa a makon daya gabata ne masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci na jihar Kano suka samar da wani kwamiti mai mutane ashirin domin lalubo hanyoyin da zasu Kare dukiyoyin su yayin zanga zangar ta lumana.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version