Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya yi fice daga jam’iyyar PDP.
Mark ya bayyana kudurinsa na ficewa daga jam’iyyar ta adawa ne a wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na mazabar sa a karamar hukumar Otukpo ta jihar Benue.
An sanya ranar 27 ga Yuni a wasikar, wadda ta bayyana bayan da kawancen jam’iyyun adawa suka amince da jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su fata Da APC, inda aka naɗa David Mark a matsayin shugaba.
Daily Nigerian Hausa