Wani sabon haɗarin kwale-kwale ya yi ajalin aƙalla mutum shida a Garin-Faji da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
A wani rubutu da shugabar hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, Zubaida Umar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce haɗarin ya auku ne a lokacin da mutum 30 suke tafiya a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ta ce sun samu labarin aukuwar lamarin ne a ranar Asabar, inda jami’anta da haɗin gwiwar jami’an hukumar agajin gaggawa ta jihar Sokoto da sojoji da sauran masu da tsaki suka kai ɗauki.
Ta rubuta cewa an ceto mutum 21 da matuƙa kwale-kwale biyu, “amma mutum shida sun rasu, sannan har yanzu ana neman mutum uku,” in ji ta, sannan ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin neman su.
Ta ce tuni mutanen garin suka birne waɗanda suka rasu, sannan ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar sufurin ruwa su tabbatar ana bin dokokin sufurin ruwa domin kare yawaitar haɗari