Wata tawaga ta musamman daga Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta isa birnin Madinah mai tsarki da ke kasar Saudiyya domin halartar jana’izar marigayi attajiri kuma dattijon kasa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Alhaji Dantata ya rasu ne a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Asabar yana da shekaru 94.
Tawogar gwamnatin tarayya ta isa Madina don jana’izar Dantata
Tawagar ta tashi daga Najeriya ne da yammacin Lahadi, inda ta isa Madinah da safiyar Litinin domin karbar gawar marigayin kafin jana’izar da za a gudanar daga bisani a ranar Litinin.
Tawagar na karkashin jagorancin Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Daga cikin tawagar akwai Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Prince Lateef Fagbemi, SAN; Ministan Watsa Labarai Alhaji Mohammed Idris, da kuma karamin Ministan Harkokin Gidaje , Hon. Yusuf Abdullahi Ata.
BUK Mourns Passing of Alhaji Aminu Alhassan Dantata
Har ila yau, cikin tawagar akwai fitattun malamai da jagororin addinin Musulunci, irinsu Dr. Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Khalifa Abdullahi Muhammad, limamin masallacin Dantata da ke Abuja.
Tawagar na aiki tare da ofishin jakadancin Najeriya da ke Jeddah, karkashin jagorancin Jakada Muazzam Ibrahim Nayaya, wanda ke jagorantar shirye-shiryen jana’izar da za a gudanar daga bisani a yau Litinin.
Daily Nigerian Hausa