Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da fitar da yayan kadanya
na tsawon watanni shida, domin rage safarar ɓoye-ɓoye, karfafa sarrafa kayan a cikin gida, da kuma ƙarfafa matsayi na Najeriya a kasuwar shea ta duniya.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya sanar da wannan umarni ranar Talata yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya bayyana cewa matakin zai fara aiki nan take kuma za a sake duba shi bayan wa’adin ya ƙare.
Shettima ya ce wannan mataki “ba shirin hana cinikayya ba ne,an yi shi ne domin tabbatar da cewa masana’antu a Najeriya suna aiki da cikakken ƙarfin su, don ƙirƙirar ayyukan yi, ƙara kudaden shiga ga al’umma da kuma bunƙasa fitar da kayayyaki.
“Najeriya na samar da kusan kashi 40% na shea butter a duniya, amma muna da kaso 1% kacal a kasuwar da ta kai dala biliyan 6.5. Wannan abin ba a iya amincewa da shi ba,” in ji shi. “A ɗan lokaci, wannan mataki zai iya samar da kusan dala miliyan 300 a shekara, kuma zuwa 2027, za a samu ƙaruwa sau goma. Wannan shi ne burinmu.”
Ya ƙara da cewa matakin zai sauya matsayin Najeriya daga mai fitar da yayan man kadanya kai tsaye zuwa mai fitar man kadanya, da sauran kayayyakin da aka sarrafa, yana mai nuna rawar da zai taka wajen kera masana’antu, bunƙasa karkara, da ƙarfafa mata.
Haka kuma, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa Najeriya da Brazil sun cimma matsaya wajen ba da damar shiga kasuwar Brazil da kayayyakin shea daga Najeriya a cikin watanni uku masu zuwa.
Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana matakin a matsayin mai dacewa da lokaci, yana mai jaddada cewa duk da cewa Najeriya na samar da tan metrik 350,000 na shea a kowace shekara a jihohi 30, kasar tana da kaso ƙasa da 1% a kasuwar duniya.
Masana’antun sarrafawa a Najeriya na aiki da kashi 35–50% kacal na ƙarfin su, duk da cewa ƙasar na da ƙarfin tan metrik 160,000.
Ƙasashen makwabta irin su Ghana, Burkina Faso, Mali da Togo sun riga sun ɗauki matakin hana fitar da shea a asali don kare masana’antunsu.
Sanata Kyari ya ce Najeriya na da fiye da hekta miliyan 5 na bishiyoyin shea daji, abin da ya baiwa ƙasar babbar dama ta kera kayayyaki da sarrafa su.
“Kasuwar duniya tana kan hanyar ƙaruwa daga dala biliyan 6.5 zuwa biliyan 9 nan da shekarar 2030. Najeriya za ta iya zama gaba a wannan ci gaban,” in ji shi. Ya ƙara da cewa tun da mata ne kashi 90% na masu tattara da sarrafa shea, wannan mataki kai tsaye zai ƙara karfin mata da samar da ayyukan yi a karkara.
Kyari ya ce wannan matakin zai kare kayayyakin cikin gida, rage safarar ɓoye-ɓoye, baiwa masana’antun damar aiki da cikakken ƙarfin su, kuma ya ba Najeriya damar shiga kasuwar duniya da ƙarfi.
“Ba tare da daukar mataki ba, Najeriya za ta zama cibiyar saye kawai ta masu cin gajiyar kasuwar waje, inda hakan zai jawo asarar biliyoyin dala,” in ji shi.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu na da cikakken niyya wajen tabbatar da cewa sashen shea ya zama ginshiƙin fitar da kayayyakin da ba na man fetur ba, domin bunkasa masana’antu da tattalin arzikin ƙasa.