Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja zuwa birnin Rome na kasar Italiya, domin halartar taron shugabannin kasashen Aqaba da na matakin gwamnati, wanda zai maida hankali kan matsalar tsaro da ke kara kamari a yammacin Afirka.
Gwamnan Kano Ya Sanya Hannu kan Dokar Kafa Rundunar Tsaro
Taron wanda aka shirya fara shi a ranar 14 ga watan Oktoba, zai hada da shugabannin kasashen duniya, da manyan jami’an leken asiri da na soji daga sassan Afirka, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da masu zaman kansu, domin tattaunawa kan matsalolin tsaro da suka kunno kai a yankin.
Shirin na Aqaba, wani shiri na yaki da ta’addanci da aka kaddamar a shekarar 2015 wanda Sarkin Jordan Abdullah na biyu na kasar Jordan da Italiya ke jagoranta, na da nufin karfafa hadin gwiwa a duniya kan yaki da ta’addanci.
Tattaunawar da za a yi a taron, za ta ta’allaka ne kan yaduwar hanyoyin sadarwa na ‘yan ta’adda, da alakar da ke tsakanin shirya laifuka da ta’addanci, da kuma yadda ake samun ci gaba tsakanin ‘yan ta’addar da suka samo asali daga kasa a yankin Sahel da kuma masu fashin teku a mashigin tekun Guinea.
Gwamnatin Kano Ta Nemi Karin Guraben Aiki a Hukumomin Tsaro
Ana sa ran mahalarta taron za su yi musayar ra’ayi kan yanayin tsaro na yanzu, da inganta hadin gwiwa tsakanin abokan huldar yanki da na kasa da kasa, da kuma tsara dabarun dakile barazanar kasa da teku.
Taron zai kuma binciko sabbin hanyoyin yaki da tsattsauran ra’ayi ta yanar gizo da kuma wargaza hanyoyin sadarwa na zamani da ake amfani da su wajen daukar ‘yan ta’adda da farfaganda.
A yayin zamansa a birnin Rome, shugaba Tinubu zai kuma tattauna da wasu shugabannin kasashen duniya kan hanyoyin hadin gwiwa don magance matsalar rashin tsaro a yammacin Afirka.
Zai samu rakiyar karamin ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu; Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar; Mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu cikin wasu da dama.

