A wani yunkuri na kara wayar da kan matasa game da muhalli, shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (Kano-ACReSAL) ya gudanar da gangamin ilimantar da dalibai kan sauyin yanayi a makarantar Yan Mata kimiyya da fasaha karkashin shirin sa na “Catch Them Young”.
Wannan gangami na daga cikin mataki na biyu na aikin wanda ke nufin hada dalibai, malamai da masana muhalli domin tattaunawa kan sauyin yanayi da kuma yadda matasa za su taka rawa wajen dakile matsalolinsa.
World Bank Delegation Visits Kano for ACReSAL Project Review
Shugaban shirin Dr. Abdulhamid Bala, ya bayyana sauyin yanayi a matsayin babban kalubale da duniya ke fuskanta.
“Sauyin yanayi barazana ce mai dorewa ga dorewar duniya. Dole ne martaninmu ya zama mai tsari kuma da sauri,” in ji shi.
Dr. Bala ya ce sun mayar da hankali kan yara makarantun sakandare ne domin su ne jagororin gobe.
“Mun kaddamar da shirin Catch Them Young ne domin mu fara gina tunaninsu tun da wuri. Dole ne mu koya musu kyawawan dabi’u na kula da muhalli tun suna kanana,” in ji shi.
Ya kuma bukaci daliban su zama jakadun muhalli a inda suke, yana mai yabawa da matakin gwamnatin jihar na komawa amfani da hasken rana.
“Sauya ofisoshi da fitilun titi zuwa na hasken rana wani babban ci gaba ne. Muna so ku yada wannan ilimi domin kare muhallinku ko ina kuka samu kanku,” ya kara da cewa.
Kano-ACReSAL Conducts Sensitisation for Resettlement Plan
Masana daga Jami’ar Bayero Kano (BUK) da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST) Wudil ne suka jagoranci zaman koyarwa a yayin taron.
Dr. Ummi Khaltum Muhammad daga Centre for Dryland Agriculture da Farfesa Muhammad Alhaji sun yi bayani kan ilimin sauyin yanayi, illolinsa da hanyoyin da za a bi don tinkarar matsalolin da ke tattare da shi.
A yayin gangamin, an kafa Kungiyar Kare Muhalli a makarantar domin jagorantar ayyukan muhalli tsakanin dalibai da ma al’ummar da ke zagaye da su.
Baya ga haka, tawagar gangamin ta baiwa makarantar shuke-shuke na itatuwan ‘ya’yan itatuwa guda 100 domin su dasa su, sannan daliban kungiyar su kula da su. Haka kuma, an raba takardun ilmantarwa kan sauyin yanayi da kare muhalli ga dalibai da malamai.