Close Menu
PARADIGM NEWS
    Facebook X (Twitter) Instagram
    • Home
    • Privacy Policy
    Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
    PARADIGM NEWS
    • Home
    • Features

      I’ll dress elegantly for a week, lady vows as Kano women storm markets

      March 29, 2025

      Dr. Abdullahi Umar Ganduje’s Legacy of Progress and Excellence

      December 25, 2024

      The rise and fall of Faruk Lawan: A lesson in power and intrigues

      December 17, 2024

      Will The Axing of Zakirai Make Education Great In Kano

      December 17, 2024

      Harmattan Brings Boom to Tea, Noodle, Bean Cake Sellers in Kano

      December 15, 2024
    • News
      1. Local
      2. National
      3. International
      4. View All

      NGO Empowers 50 GBV Survivors in Kano

      July 29, 2025

      KNSG Launches Safe Space for Women Battling Drug Addiction

      July 22, 2025

      Rescue Efforts End in Tragedy as Four Drown in Kano Waterway

      July 19, 2025

      Kano Assembly Denies Investigating ALGON Chair Hajiya Sa’adatu

      July 18, 2025

      NHIA, NSITF Unite to Bridge Gaps in Workers’ Welfare Schemes

      July 27, 2025

      Justice and Dignity at Heart of Nigeria’s Correctional Reforms- Minister

      July 27, 2025

      Renewed Hope Estate Kano Set for Tinubu’s Commissioning

      July 25, 2025

      Empower Youth to Drive Natl Development — NPC Tells Nigerians

      July 25, 2025

      Trump to Withdraw U.S. from UNESCO Again, Slams “Woke”

      July 29, 2025

      UN Summit: Africa Calls for Urgent Action on Global Food Crisis

      July 29, 2025

      Tinubu’s Green Diplomacy in Action as Nigeria Donates Cashew to Ethiopia

      July 28, 2025

      Just in: Saudi Arabia’s Sleeping Prince Dies After 19 Years in Coma

      July 20, 2025

      UNICEF Appoints Wafaa Saeed as New Country Representative in Nigeria

      July 29, 2025

      Jigawa State Disburses Over ₦1.5 Billion to 569 Retirees

      July 28, 2025

      KNHA Recommends Revocation of 5km Gabasawa Road Project

      July 28, 2025

      Minister Assures Swift Evacuation of Nigerians Abandoned in CAR

      July 27, 2025
    • Politics

      Just in : Atiku Quits PDP, Blames Party’s New Direction

      July 16, 2025

      Sule Lamido Backs Opposition Coalition Under ADC

      July 15, 2025

      Ringim Blames Sule Lamido, Not Wike, for PDP Crisis

      July 13, 2025

      Commissioner Waiya Endorses Women’s Political Representation

      July 7, 2025

      Gauta Club Gets 14 New Patrons as Waiya Champions Inclusive Politics

      July 5, 2025
    • Conflict

      Kadpoly Retiree faults Committee, Demolition Of Property

      March 27, 2025

      President Tinubu Declares State of Emergency in Rivers State

      March 18, 2025

      El-Rufai Defends Najaatu Muhammad Against Ribadus Denials

      February 5, 2025

      Tinubu’s Corruption Saga: Najaatu-Ribadu Feud Takes Center Stage

      February 5, 2025

      Kano Inaugurates Committee to Investigate Rimin Zakara Dispute

      February 3, 2025
    • More
      • Analysis
      • Business
      • Crime
      • Cultural events
      • Economy
      • Education
      • Editorial
      • Entertainment
      • Environment
      • Fashion
      • Health
      • Lifestyle
      • Personality profile
      • Science
      • Sports
      • Technology
    • Hausa

      Biza don Haihuwa:Amurka Ta Sanya Sabon Sharadi Ga Yan Najeriya

      July 29, 2025

      Likitoci a Legas Za Su Fara Yajin Aiki na Kwana Uku

      July 28, 2025

      PDP Ta Bukaci Fayose Ya Fice Daga Cikin Jam’iyyar

      July 28, 2025

      NYSC Ta Sha Kaye a Kotu Kan Haramta Siket Ga ‘Yan Mata

      July 28, 2025

      Labari Cikin Hotuna:Aisha Buhari ta Koma KD Domin yin Takaba

      July 28, 2025
    Subscribe
    PARADIGM NEWS
    Home » ‘Yan Kasuwar Kwari sun yi kira da a magance yawan haraji a Kano
    Hausa

    ‘Yan Kasuwar Kwari sun yi kira da a magance yawan haraji a Kano

    EditorBy EditorMay 17, 2024Updated:August 5, 2024No Comments3 Mins Read
    Facebook Twitter Telegram WhatsApp
    IMG 20240517 WA0007

    Shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan Kasuwar Kantin Kwari Alhaji Ishaq Alkasim wanda aka fi sani da Balarabe Tatari yayi kira ga gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf daya magance matsalar yawan karbar haraji wato multiple taxation a turance.

    Balarabe wanda Kuma shine shugaban gidajen Kantin Kwari da wasu kungiyoyin yan Kasuwa ya bayyana cewa yawan karbar haraji kashi kashi wato multiple taxation daga hannun ‘yan kasuwa ya durkusar da harkokin kasuwanci a jihar.

    RELATED: Daruruwan yan tebura a kasuwar kantin kwari sun rasa guraben sana’ar sanadiyar rusau din KANUPDA

    Ad 4

    Ya ce a yanzu haka suna biyan haraji har kashi hudu banda sauran matsalolin da ke cigaba da addabar su.

    Shugaban ya nuna takaicin sa a bisa gine musu hanyar dake kusa da gidan Garban Bichi da wasu gine gine da kuma kwantena da teburan karfe sa ake sakawa a wasu sassan Kasuwar.

    Balarabe yace gine gine a hanyoyin ruwa ko titunan Kasuwar na da matukar illa wanda ka iya haifar da ambaliyar ruwa da kuma cunkoso cikin wasu da dama.

    Ad 3

    Ya kuma bayyana cewa teburan karfe ka iya haifar da matsaloli masu taron yawa wanda a duk lokacin da aka samu akasi zai yi wuya a iya dauke su cikin sauki ba kamar na katako ba.

    Dangane da batun hauhawar farashin tufafi Balarabe ya alakanta hakan ne da wadansu gine gine da gwamnatin da ta shude tayi tare da sanya makudan kudade ga ‘yan kasuwar a matsayin kudin haya,da matsalar canjin kudaden ketare da tsarin rage kudade a hannun mutane na cashless policy da gwamnatin baya ta bijiro da shi sai jami’an fasakwauri da suke tare ‘yan kasuwa musamman wadanda suke sarin kaya izuwa wadansu garuruwan.

    Ash Noor

    “A baya idan mutum ya bude Kantin sa tun safe zai fara ciniki wani lokacin idan yamma ta yi sai ya rika rokon jama’a cewa lokacin tashi yayi zai tafi gida amma a yanzu haka wani layin idan ka shiga sai dai ka tarar ‘yan kasuwa na hira ko buga game a waya ko chatting saboda karancin masu siyayya”

    Shugaban ya ce tun bayan zaben shi a matsayin Shugaban Kasuwar sun Kai takardar korafi ga gwamnatin jihar Kano akan matsalar yawan karbar haraji da gine gine ba bisa ka’ida ba inda Kuma sun tattauna so daya da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kano.

    “Tun a baya mun Kai takardun korafi da dama ga majalisar dokokin jihar Kano da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta anti corruption ma’aikatar Kasuwanci da gwamnatin jihar Kano da rundunar ‘yan sandan Kano cikin wasu da dama”

    Ya kuma yi tsokacin cewa ‘yan kasuwar ta Kwari na daya daga cikin wadanda suka yi fitar dango wajen kadawa gwamnatin Engineer Abba Kabir Yusuf kuri’a saboda suna yi mishi kyakkawan zato.

    “Mai girma Gwamna ina rokon da ayi duba na tsanaki akan irin yadda Yan kasuwa suka yi tururuwa wajen zuwa cibiyoyin zabe. Akwatunan zaben dake cikin Kantin Kwari na cike da tarin kuri’un mu Wanda mun yi hakan ne saboda rashin adalcin da aka yi mana a baya Kuma Muna tunanin zaka share mana hawaye”

    Balarabe Tatari ya Kara jaddada aniyar sa wajen kare daraja da dukiyoyin ‘yan kasuwa domin maidowa Kano martabar ta na babbar cibiyar Kasuwancin nahiyar Africa.

     

     

    Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram WhatsApp

    Related Posts

    Biza don Haihuwa:Amurka Ta Sanya Sabon Sharadi Ga Yan Najeriya

    July 29, 2025

    Likitoci a Legas Za Su Fara Yajin Aiki na Kwana Uku

    July 28, 2025

    PDP Ta Bukaci Fayose Ya Fice Daga Cikin Jam’iyyar

    July 28, 2025

    NYSC Ta Sha Kaye a Kotu Kan Haramta Siket Ga ‘Yan Mata

    July 28, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Editors Picks

    UNICEF Urges Kano to Extend Maternity Leave, Invest More in MNCH

    July 29, 2025

    2025 MNCHW: Kano Distributes 6,000 Delivery Packs, 500 C/S Kits

    July 29, 2025

    UNICEF Appoints Wafaa Saeed as New Country Representative in Nigeria

    July 29, 2025

    Kano Unveils Climate Change Policy, Targets 5M Tree Planting

    July 29, 2025
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    Hajaj Albait 2
    © 2025 PARADIGM NEWS
    • Home
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.