Shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan Kasuwar Kantin Kwari Alhaji Ishaq Alkasim wanda aka fi sani da Balarabe Tatari yayi kira ga gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf daya magance matsalar yawan karbar haraji wato multiple taxation a turance.

Balarabe wanda Kuma shine shugaban gidajen Kantin Kwari da wasu kungiyoyin yan Kasuwa ya bayyana cewa yawan karbar haraji kashi kashi wato multiple taxation daga hannun ‘yan kasuwa ya durkusar da harkokin kasuwanci a jihar.

RELATED: Daruruwan yan tebura a kasuwar kantin kwari sun rasa guraben sana’ar sanadiyar rusau din KANUPDA

Ya ce a yanzu haka suna biyan haraji har kashi hudu banda sauran matsalolin da ke cigaba da addabar su.

Shugaban ya nuna takaicin sa a bisa gine musu hanyar dake kusa da gidan Garban Bichi da wasu gine gine da kuma kwantena da teburan karfe sa ake sakawa a wasu sassan Kasuwar.

Balarabe yace gine gine a hanyoyin ruwa ko titunan Kasuwar na da matukar illa wanda ka iya haifar da ambaliyar ruwa da kuma cunkoso cikin wasu da dama.

Ya kuma bayyana cewa teburan karfe ka iya haifar da matsaloli masu taron yawa wanda a duk lokacin da aka samu akasi zai yi wuya a iya dauke su cikin sauki ba kamar na katako ba.

Dangane da batun hauhawar farashin tufafi Balarabe ya alakanta hakan ne da wadansu gine gine da gwamnatin da ta shude tayi tare da sanya makudan kudade ga ‘yan kasuwar a matsayin kudin haya,da matsalar canjin kudaden ketare da tsarin rage kudade a hannun mutane na cashless policy da gwamnatin baya ta bijiro da shi sai jami’an fasakwauri da suke tare ‘yan kasuwa musamman wadanda suke sarin kaya izuwa wadansu garuruwan.

A baya idan mutum ya bude Kantin sa tun safe zai fara ciniki wani lokacin idan yamma ta yi sai ya rika rokon jama’a cewa lokacin tashi yayi zai tafi gida amma a yanzu haka wani layin idan ka shiga sai dai ka tarar ‘yan kasuwa na hira ko buga game a waya ko chatting saboda karancin masu siyayya”

Shugaban ya ce tun bayan zaben shi a matsayin Shugaban Kasuwar sun Kai takardar korafi ga gwamnatin jihar Kano akan matsalar yawan karbar haraji da gine gine ba bisa ka’ida ba inda Kuma sun tattauna so daya da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kano.

Tun a baya mun Kai takardun korafi da dama ga majalisar dokokin jihar Kano da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta anti corruption ma’aikatar Kasuwanci da gwamnatin jihar Kano da rundunar ‘yan sandan Kano cikin wasu da dama”

Ya kuma yi tsokacin cewa ‘yan kasuwar ta Kwari na daya daga cikin wadanda suka yi fitar dango wajen kadawa gwamnatin Engineer Abba Kabir Yusuf kuri’a saboda suna yi mishi kyakkawan zato.

Mai girma Gwamna ina rokon da ayi duba na tsanaki akan irin yadda Yan kasuwa suka yi tururuwa wajen zuwa cibiyoyin zabe. Akwatunan zaben dake cikin Kantin Kwari na cike da tarin kuri’un mu Wanda mun yi hakan ne saboda rashin adalcin da aka yi mana a baya Kuma Muna tunanin zaka share mana hawaye”

Balarabe Tatari ya Kara jaddada aniyar sa wajen kare daraja da dukiyoyin ‘yan kasuwa domin maidowa Kano martabar ta na babbar cibiyar Kasuwancin nahiyar Africa.

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version