Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a cikin wani harin fashi da makami da kuma yunƙurin kisan kai da ya auku a Bera Estate, Chevron, Lagos a ranar 19 ga watan Agusta, 2025.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 20 ga Satumba, 2025.
Kano Police Arrest 107 Suspects, Recover Weapons, Drugs
Ya bayyana sunayen waɗanda ake zargi da Mathew Adewole (25), mazaunin Na’ibawa Quarters Kano, da kuma Mukhtar Muhammad (31), mazaunin Unguwa Uku Kano.
A cewar sanarwar, Adewole ya amsa cewa shi ne ya kai wa wani mazaunin Lagos mai suna Lil-Kesh hari da adda, inda ya ji masa mummunan rauni a wuya, a yayin da yake ƙoƙarin yin fashi.
Bayan haka kuma, ya tilasta wa wanda abin ya faru da shi ya tura Naira miliyan 2.12 zuwa asusun bankin abokin harkallarsa, Mukhtar Muhammad.
Sanarwar ta ƙara da cewa kama mutanen ya biyo bayan sahihin bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, na ƙarfafa aikin leƙen asiri da haɗin gwiwar al’umma wajen yaƙi da aikata laifuka.
Akwa Ibom Police Records Major Breakthroughs in Crime-Fighting
Rundunar ta mika waɗanda ake zargi ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Lagos domin ci gaba da bincike da gurfanarwa a kotu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, ya gode wa jama’a bisa haɗin kai, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

