Aƙalla mutane 24 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan da wata mata ta kai kunar bakin wake a daren jiya Juma’a a karamar hukumar Konduga da ke jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Borno, ASP Nahun Daso, wanda ya tabbatar da hakan a ranar Asabar, ya ce matar ta tayar da wani abun fashewa a wani wajen cin abinci inda mutane da dama suka taru don sayen abinci.
Mr Daso ya bayyana cewa fashewar ta raba jikin matar gida-gida, inda kawai aka samu kanta ne daga wajen harin.
“Bayan faruwar lamarin, tawagar haɗin gwiwa da ta haɗa da sashen ‘yan sanda mai kula da abubuwan fashewa, sojoji, ‘yan sa-kai na CJTF da masu farauta na gari sun je wajen da abin ya faru,” inji shi.
Kakakin ya ƙara da cewa an killace yankin kuma an gudanar da bincike sosai don gano ko akwai wasu na’urorin fashewa da ke makare, amma ba a samu wani ba.
“An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), inda ake ci gaba da kula da su, yayin da gawarwakin waɗanda suka mutu aka adana su a dakin ajiye gawarwaki na asibitin.
Daily Nigerian Hausa