Managing Daraktan Hukumar KAROTA ta Jahar Kano, Alhaji Faisal Mahmud Kabir ya yi alwashin tsabtace harkokin Sufirin manyan Motocin Safa-Safa (Luxurious)wandake gudanar da harkokin sufuri zuwa Kudancin kasar nan.
Hon. Faisal Mahmud ya baiyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Shugabannin Kungiyar Tashar Luxurious wanda suka kai masa ziyarar bangirma a ofishin sa.
Manajan Daraktan ya yi kira ga ‘yan Kungiyar dasu taimakawa gwamnati wajen sa ido bisa shige da ficin kayyakin da ake dorawa a Motocin Safa-Safa da kuma masu fasakwaurin kananan yara zuwa Kudancin kasar nan.
Ya godewa ‘yan Kungiyar bisa ziyarar da suka kawo masa, inda Ya tabbatar musu da hadin kai da kuma taimakon Hukumar KAROTA a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Manajan Daraktan ya kara da cewar Hukumar KAROTA zata ci gaba da tuntubar masu hannu da shuni da Hukumomin gwamnati duba yiwuwar zuba jari a harkokin Sufirin manyan Motocin Safa-Safa.
Tunda farko, Sakataren Kungiyar ta ‘Yan Luxurious ta Jahar Kano, Alh Auwalu Abdullahi yace sun kawo ziyarar ne don neman sa albarka daga Manajan Daraktan na Hukumar KAROTA.
Alh Auwalu Abdullahi ya jaddada bukatar dake akwai ga Gwamnatin Jahar Kano da masu hali su shigo harkar Sufirin manyan Motocin Safa-Safa don kara bunkasa ta da kuma kare mutunci da tsaron rayuka da dukiyin al’ummar Jahar Kano.