Tun bayan da ƴansandan jihar Jigawa suka kama wani matashi bisa zargin aikata fyaɗe ga wata yarinya mai shekara takwas, ya sa jama’a ke ta neman sanin hanyoyin gano yadda ake cin zarafin ƙananan yara.

Kokarin Yaki Da Dabi’un Cin Zarafun Mata A Kaduna Da Yadda Kwalliya Ke Biyan Kudin Sabulu

BBC ta tuntuɓi barrister Aisha Ali Tijjani wadda lauya ce mai zaman kanta a birnin Kano, da Dakta Muhammad Hadi Musa, wanda malami ne a tsangayar nazarin laifuka a Jami’ar Open University ta Najeriya wanda BBC ta tuntuɓa a kwanakin baya, dangane da matsalar inda kuma suka zayyana hanyoyi guda huɗu na kaucewa faruwar cin zarafi ga yara mata da maza.

Jigawa Gov Offers Support to Assaulted Minor, Warn Against GBV

Dakta Muhammad Hadi Musa da Barrister Aisha sun amince cewa kowa zai iya zama abin zargi a yanayin da ake ciki yanzu duk wani ɗa namji ka iya zama abin zargi – walau babba ko yaro, na kusa ko na nesa.

AFA Workshop Unites Media Against Sexual Harassment in Nigeria

“Lallai babu wani rukunin mutanen da za ka ce su ne suke aikata laifukan fyaɗe. Kowa na iya yi tunda dai al’amarin shaiɗanci ne da lalacewa. Mun samu yara da matasa da tsofaffi duk da laifin aikata fyaɗe.” In ji barrister

Womanifesto demands Justice for Late Olufunmilayo Oluwemimo

Dakta Muhammad Hadi Musa, wanda malami ne a tsangayar nazarin laifuka a Jami’ar Open University ta Najeriya, wanda kuma ya bayyana cewa akwai buƙatar iyaye su rinƙa bincike ko tuhuma a duk lokacin da suka ga wani kusanci ko kuma soyayya ta yi yawa tsakanin malami ko wani majiɓincin lamari ko daga aboki ko daga ƙawa, ko daga amarya a makwafta ko wani babban mutum a makwafta.

Dakta Muhammad ya ce akwai wani bincike da suka yi a kwanakin baya inda suka gano yadda wani shugaban makaranta ya rinƙa lalata da wani yaro na makarantarsa ta firamare a Kano wanda har shugaban makarantar ya saya masa waya da agogo.

Kotun Daukaka Kara ta kama Trump da laifin Cin Zarafin Yarjarida

Ya ce ko da mahaifin yaron ya ga haka sai ya tuntuɓi shugaban makarantar domin jin dalilin da ya sa ya saya wa yaron agogo sai ya ce don yaron yana da ƙoƙari ne amma mahaifin yaron ya san ƙoƙarin ɗansa bai kai har ya rinƙa zuwa na ɗaya a makaranta ba.

Dakta Muhammad ya bayyana cewa ya kamata a kowane lokaci a rinƙa lura da irin wannan soyayya domin gano gaskiyar lamari.

Barrister Aisha ta ce babbar matsalar da ke janyo yara kan fuskanci cin zarafi shi ne yadda iyaye ke sakaci da al’amuransu.

“Abin mamaki sai ka ga iyaye sun yi biris da ƴaƴansu kamar ba su ne suka haife su ba ko kuma don sun yi musu yawa ne? Musamman ma a sababbin unguwanni sai ka ga an tura shi kaɗai ya tafi wasa waje kuma a wajen nan akwai mugwayen mutanen da ke jiran irin wannan dama.”

Ta ƙara da cewa duk mahaifan da suke sakaci da wurin da yaransu suke a kowane wayewar gari to fa tabbas sun cikin hatsarin fuskantar fyaɗe da duk sauran nau’in cin zarafi.

“Hakan ne ma ke janyo mugaye su daɗe suna cin zarafin yaran ba tare da uwa ko uba ya fahimci hakan ba. Amma idan ana lura to babu yadda za a yi a kasa ganewa.” In ji barrister

Wani abu da yanzu iyaye ba kasafai suke yi ba shi ne ilmantar da yara dangane da illolin kusantar mugayen mutane.

Dangane da wannan hakan ne, a kwanakin baya BBC ta tuntuɓi Dakta Muhammad Hadi Musa, wanda malami ne a tsangayar nazarin laifuka a Jami’ar Open University ta Najeriya, inda ya bayyana cewa akwai buƙatar iyaye su taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan ƴayansu domin gudun faruwar waɗannan munanan lamura.

Ya bayyana cewa jama’a kan saki jiki ba tare da ɗaukar mataki ba sai wani abin ƙi ya faru tukuna sai a tashi tsaye a yi ta magana a kai.

Ya bayyana cewa wayar da kan yara da gargaɗinsu da tsoratar da su yana taimakawa matuƙa.

Ya bayyana cewa yana da kyau a rinƙa kiran yaro ko yarinya ana faɗa musu da cewa “Idan ka ga mutum zai baka alawa kada ka karɓa ka gudu, idan baka san mutum ba ya kiraka kan babur ko Adaidaita Sahu ka gudu ko ka tafi inda manya suke ka tsaya a kusa da su.

“Idan wani ya zo zai riƙe maki hannu kada ki yarda za ki yi ciki, idan kika yi ciki yanka ki za a yi mutuwa za ki yi, kin ga yadda ake yanka rago? ana riƙe maki hannu ciki za ki yi,” in ji shi.

Ya ce ya kamata a rinƙa irin wannan tsoratarwa ga yara domin yana taimakawa sosai. Ya ce kuma akwai buƙatar yara su san al’aurar su da sauran sassan jikinsu inda ya ce shi ma hakan yana da matuƙar muhimmanci.

BBC HAUSA

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version