Manchester United na shirin gogayya da Paris St-Germain a kan dan wasan gaba na Napoli da Georgia Khvitcha Kvaratskhelia, mai shekara 23. (L’Equipe )
Haka ita ma Liverpool kila za ta nemi sayen Kvaratskhelia idan har Napoli ta ba shi damar tafiya a wannan watan. (Athletic), external
West Ham ta nemi bayani a kan ko za ta iya samun Marcus Rashford, inda take son karbar aronsa daga Manchester United. (Talksport)
Haka su ma kungiyoyin gasar Italiya – Serie A – AC Milan da Como na sha’awar sayen dan wasan na Ingila domin taka musu leda a sauran lokacin da ya rage na wannan kakar. (Gianluca Di Marzio)
Wasu fitattun ‘yan wasan Bournemouth na daukar hankalin manyan kungiyoyin Premier, – ‘yan wasan su ne, Illia Zabarnyi, Milos Kerkez, Antoine Semenyo da kuma Dean Huijsen, wadanda dukkaninsu Chelsea, da Newcastle da Liverpool ke so. (The i)
Manchester United ta bi sahun Arsenal wajen neman dan gaban Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, daga Brentford. (Mirror)
Manchester City na tattaunawa don sayen matashin dan baya Vitor Reis dan Brazil mai shekara 18 daga Palmeiras. (Athletic)
Nottingham Forest ta nemi bayani kan ko za ta samu aron dan wasan tsakiya na Juventus, Douglas Luiz, na Brazil mai shekara 26,, wanda kuma Manchester United, da Manchester City da kuma Fulham duka suna sonshi. (Mail)
Newcastle na sa ido a kan mai tsaron ragar Southampton da Ingila, Aaron Ramsdale, mai shekara 26 (Sun)
Borussia Dortmund ta tuntubi Manchester City a kan matashin dan bayanta, Max Alleynem, dan Ingila mai shekara 19. (Fabrizio Romano)
BBC HAUSA