Fitaccen malamin addinin Musulunci daga Zimbabwe, Mufti Ismail Ibn Menk, ya bayyana alhini da kaduwa matuka bisa rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, yana mai cewa labarin mutuwarsa ya taba zuciyarsa har ya zubar da hawaye.
Tinubu Confirms Buhari’s Death, VP Shettima to Escort Body From Uk
Mufti Menk ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a da), jim kadan bayan bayyana mutuwar Buhari.
“Rasuwar gwarzo, tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari – Allah Ya jikansa – ta sa na zubar da hawaye!” in ji malamin.
Mufti Menk ya yaba wa marigayin bisa ladabinsa da tsayuwarsa kan addini, yana mai cewa Buhari mutum ne mai kamun kai da gaskiya wanda ya yi wa kasarsa hidima cikin amana da tsoron Allah.
“Mutum ne mai gaskiya wanda bai taɓa barin sallah ba. Mumini ne na gaskiya kuma mai ladabi wanda ya yi iya kokarinsa wajen hidimtawa al’umma. Sunansa na nuni da gaskiya da rikon amana,” in ji shi.
Breaking: Former Nigerian President Buhari Passes Away in London
A cikin wani bangare mai motsa zuciya, Mufti Menk ya ce halayen Buhari sun taimaka masa wajen ganin ‘yan Najeriya da idon basira.
“Shi ne daya daga cikin mutanen da suka sa na sauya tunani game da ‘yan Najeriya, har na kara darajarsu a zuciyata,” ya bayyana.
Malamin ya rufe sakonsa da addu’o’i na neman rahama da gafara ga Buhari, tare da ta’aziyya ga iyalansa da al’ummar Najeriya baki daya.
“Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya ba shi matsayi mafi girma a Aljanna. Aameen. Allah Ya saukaka wa iyalansa, abokansa da al’ummar Najeriya.”
Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti da ke Landan bayan fama da doguwar rashin lafiya. Rasuwarsa ta jawo martani da jimami daga ciki da wajen Najeriya.