Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta ta yin aiki tare da shugabannin kananan hukumomi domin aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a yankunansu.
Kwamishinan Ma’aikatar Ci gaban Kauyuka da Al’ummomi, Alhaji Abdulƙadir Abdussalam, ne ya bayyana haka yayin ziyarar aiki da ya kai Ƙaramar Hukumar Gwarzo.
KH Gwarzo Ta Raba Gidan Sauro 189,600 Don Yaki da Maleriya
Ya bayyana cewa ziyarar na da nufin sauraron bukatun al’ummomin karkara kan irin ayyukan ci gaba da suke son gwamnati ta aiwatar, bisa umarnin Gwamnatin Jihar Kano ga kwamishinoni su ziyarci dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.
Alhaji Abdulƙadir ya fara ziyarar ne da ganawa da Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano, Alhaji Bello Abubakar, a fadarsa da ke Gwarzo.
Ya ce haɗin gwiwar zai mai da hankali kan muhimman fannoni kamar:
Gina hanyoyi da wasu muhimman gine-gine
Inganta harkar kiwon lafiya
Samar da ruwan sha mai tsafta
Ci gaban noma da ilimi
Wayar da kan jama’a da samar da wutar lantarki a karkara
Sabuwar Daraktar Harkokin Ma’aikata Ta Gwarzo Ta Kama Aiki
Kwamishinan ya kira shugabannin unguwanni, masu rike da mukaman gargajiya, kungiyoyin al’umma, matasa da dalibai da su gabatar da bukatunsu ta hannun kansilolinsu.
Ya kuma bukaci kowace bukata ta kasance da gajeriyar bidiyo da ke gabatar da kansu tare da bayanin aikin da suke so a aiwatar, domin gabatarwa gaban Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho Gwarzo, wanda Mataimakinsa, Hon. Abdulmumin Garba Lakwaya, ya wakilta, ya nuna farin ciki da ziyarar tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar, musamman amincewar gyara rijiyoyin burtsatse 143 a fadin ƙaramar hukumar don inganta samar da ruwa.
Daga cikin manyan bakin da suka yi jawabi akwai:
Alhaji Musbahu Dadawi – Babban Sakatare, Ma’aikatar Ci gaban Kauyuka
Hajiya Rukayya Umar – Babbar Mataimakiyar Musamman ga Gwamna
Alhaji Ibrahim Garba Aminu (Kofar Na’isa) – Shugaban Kwamitin Ayyukan Sa-kai na Jihar
Kwamishinan ya kuma mika kyautar musamman ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwarzo tare da daukar hoto na tunawa.
Taron ya samu halartar kansilolin da aka zaba da na nada, Sakatare na Ƙaramar Hukuma, shugaban majalisar, kungiyoyin matasa da dalibai, ƙungiyar masu bukata ta musamman, jami’an tsaro, da sauran shugabanni na al’umma.