Gwamnatin jihar Kano ta yi martani ga hukumomin tsaron da suka yiwa fadar Sarkin Kano ƙawanya.
” Mun wayi gari a Kano da wani abun mamaki, yadda Jami’ian tsaro suka mamaye gidan Sarkin Kano, ba tare da cewa akwia wata fargaba ta rashin zaman lafiya ko wani abu ba”.
A wata hira da Freedom Radio ta yi da sakataren Gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya ce, mamaye gidan Sarkin yunkuri ne kawai na kawo rashin zaman lafiya
Yace da suka tambaye jami’an tsaro dalilin jibge jami’an tsaro a gidan Sarkin sai suka ce musu wai umarni aka ba su daga Sama.
“Mu dai mun san an daina aiko waye daga sama, don haka muna zargi wasu ne suke son haka kai da yan Abuja domin kawo rashin zaman lafiya a jihar kano, wanda kuma gwamantin jihar Kano ba ta lamunta”. Inji Baffa Bichi
Dr. Baffa Bichi ya kara da cewa batun da ake yi na cewa za a iya yin tashin hankali a Bichi ba gaskiya ba ne, domin Mutane Bichi mutane ne masu son zaman lafiya kuma zasu karbi hakimin da sarki ya tura musu domin shi ma dan Bichi ne saboda mahaifinsa Sarki Sanusi na 1 ya yi hakimi a Bichi kuma wanda Abubakar ma yayi hakimin Bichi.
“Muna nan muna jiran Sarki ya sa wani lokacin za mu fito mu yi dafifi domin raka Sarki ya kai hakimi kasar Bichi ba tare da wata matsala ba, kuma ba zamu lamunci Abubuwan da wasu suke yi mana ba”. A cewar Baffa Bichi
Sakataren gwamnatin jihar kano ya kuma bukaci al’ummar jihar da su cigaba da zama lafiya kar su biye wa masu son tayar da hankali a jihar