Kwamitin ɗa’a da ladabtarwa da sauraron ƙorafin jama’a na majalisar dattawan Najeriya ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar kan zargin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da neman yin lalata da ita.
Kwamitin ya bayyana ƙorafin da cewa ”ya zo gaban kwamitin a mace”, saboda rashin bin ƙa’ida wajen shigar da shi.
A yayin zaman sauraron ƙorafin, shugaban kwamitin Sanata Neda Imasuen, ya karanto doka ta 40 cikin dokokin majalisar dattijai, inda ya bayyana cewa Sanata Natasha ta sanya hannu kan ƙorafin da kanta maimakon ta bai wa wani ya shigar da shi a madadinta, lamarin da ya lalace.
Ya kuma ƙara da cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin na gaban kotu a yanzu haka, wanda ya sa ba za a iya tattauna su ba kuma majalisar ba ta da hurumin sauraron su.
Tuni dai shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio ya musanta zargin cin zarafin da ƴar majalisar ta shigar kansa.
BBC HAUSA