Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure, ya bayar da tallafin kudi Naira N(480,000)ga sabbin jami’an kashe gobara ‘yan asalin karamar hukumar Tarauni guda 32, domin taimaka musu wajen gudanar da bikin yayesu bayan Kammala Horo
.Shugaban ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin sabbin jami’an kashe gobarar ‘yan asalin karamar hukumar Tarauni da suka Sami aikin karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir yusuf.
Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure ya bayyana Jin dadin sa da ziyarar tare da yabawa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir yusuf a bisa yadda ya dauki ma’aikatan kashe gobara.
NAHCON Ta Tabbatar da Tsaro Bayan Gobara a Masaukin Alhazai
Ya Kuma bayyana wannan mataki na gwamnatin jihar, a matsayin Wanda ya dace da manufar samar da ayyukan yi ga matasa da kuma bunkasa fannin tsaro da agajin gaggawa a fadin kananan hukumomi arbain da hudu.
Shugaban karamar hukumar ta Tarauni Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad sekure yayi kira a garesu dasu rike aikinsu bisa gaskiya da rikon Amana da jajircewa.
A jawabinsa Mai rikon Daraktan Mulki da kudi na karamar hukumar Tarauni kwamared Bello Hassan Durimin zungura ya yabawa shugaban karamar hukumar Tarauni bisa yadda yake kokari wajan kawo aiyyukan cigaba tare da tallafawa matasan yankin.
Mutane 24 Sun Rasu A Gobarar Los Angeles Ta Kasar Amurka
Ya Kuma kara da cewa wannnan tallafin
da ya baiwa sabbin jami’an kashe gobarar ‘yan asalin karamar hukumar Tarauni yayi abun da ya dace domin karfafa gwiwar matasa domin su damar kammala horonsu cikin kwanciyar hankali da jin dadi.