Gobara ta tashi a wani masaukin alhazan Nijeriya a Makka a ranar Asabar, a cewar Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON).
NAHCON ta ce gobarar ta tashi a wani otal mai suna Imaratus Sanan a titin Shahr Mansur a birnin Makka ranar Asabar da misalin karfe 12 na rana, kamar yadda sanarwar hukumar ɗauke da sa hannaun Mataimakiyar Darakta mai kula da yaɗa Labarai Fatima Sanda Usara ta bayyana.
Read also: Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa Bayan Rikici Tsakanin Matuka
NAHCON Ta Shirya Taron Masu Ruwan Da Tsarki Akan Hajjin Bana
“Otal din masaukin alhazai 484 ne na jirgin yawo daga kamfanin shirya tafiye-tafiye shida. Muna gode wa Allah, babu asarar rai, kuma dukkan alhazan suna Mina cikin kwanciyar hankali,” a cewar sanarwar.
Hajiya Fatima ta ce tuni hukumomin kashe gobara na Saudiyya suka kashe wutar ba tare da ta cinye otal din ba baki ɗaya.
Read also: ACSITE Advocates Formal Education, Support for Islamic Schools
Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman tare da wasu jami’an hukumar sun ziyarci otal din don ganin irin ɓarnar da gobarar ta yi.
NAHCON Ta Sanar Da Kudin Kujerar Hajjin Bana
“Tuni Farfesa Abdullahi ya yi umarnin mayar da alhzan gidan wani masaukin,” in ji sanarwar.
Read also: Hajj 2027: NCAA, Airlines, NAHCON Tackle Airlift Challenges
Shugaban na NAHCON ya kuma yi alƙawarin yin aiki tare da kamfanonin shirya tafiye-tafiyen da suka kai alhazan da nufin ba su taimakon da ya kamata.
TRT Afrika Hausa

