Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta aika wa mawaki Tijjani Gandu da takardar gayyata kan zargin karya dokokin Hukumar yayin sakin wata sabuwar waka.
A wata sanarwa da Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a madadin Shugaban Hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, Hukumar ta ce wajibi ne ga mawaka da marubuta su gabatar da wakokinsu ko rubuce-rubucensu kafin sakin su ga jama’a domin tantance su.
Read also: SUBEB Ta Raba Kayan Karatu Domin Ƙarfafa Zuwa Makaranta Da Wuri
Ta ce hakan na da nufin tabbatar da cewa babu kalmomi ko abubuwan da ka iya haddasa tashin hankali ko kawo barazana ga zaman lafiya a cikin al’umma.
Sanarwar ta bayyana cewa dokar da ta kafa Hukumar ta ba ta ikon tantance wakoki da sauran ayyukan da suka shafi tace fina-finai da dab’i a jihar.
Hukumar ta ce ba za ta ci gaba da kallon yadda wasu ke karya dokokinta da sunan ‘fadin albarkacin baki’ ba, tana mai jaddada cewa za ta tabbatar da bin doka da oda wajen gudanar da ayyukanta.
Read also: Kano Signs MoU with IBP on Health Financing Dashboard
Ta kuma ce za ta yi adalci ga dukkan masu ruwa da tsaki, ba tare da nuna wariya ko son kai ba.
Saboda haka, Hukumar ta bukaci Tijjani Gandu da ya amsa gayyatar da aka aika masa tare da mutunta dokokin da suka shafi harkar nishadi da dab’i a jihar.
Ta yi gargadin cewa kin amsa gayyatar na iya sa Hukumar ta dauki matakan da suka dace bisa tanadin doka.
Read also: 484 Kano Wards to Get Fully Equipped Rural Ambulances
Hukumar ta kuma yi kira ga mawaka, marubuta da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar nishadi da adabi da su ci gaba da bin dokoki da ka’idojin Hukumar.
A cewarta, bin dokokin zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, daidaito da ci gaban masana’antar nishadi da adabi a Jihar Kano.

