Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda, yana cikin koshin lafiya bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Katsina zuwa Daura a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnan, Malam Maiwada Dammallam ya fitar, hatsarin ya faru ne lokacin da wata mota ƙirar Golf ta kauce hanyarta ta buge motar da gwamnan ke ciki.
Governor Radda offers automatic employment to IKCOE Graduates
“Bayan faruwar hatsarin, an garzaya da gwamna da sauran mutanen da ke tare da shi zuwa asibitin Daura domin samun kulawar gaggawa,” in ji Dammallam. “Daga nan aka mayar da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Katsina inda ƙwararrun likitoci suka sake duba lafiyarsa, kuma suka tabbatar da cewa ba ya da wani rauni mai hatsari.”
A cikin motar gwamnan akwai Chief of Staff ɗinsa, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, Hakimin Kuraye, da kuma Alhaji Shamsu Funtua. Gwamnatin ta ce ba wanda ya samu rauni mai tsanani, sai dai ɗaya daga cikinsu da aka yi masa dinki, kuma yanzu duk suna Katsina cikin koshin lafiya.
Governor Radda offers automatic employment to IKCOE Graduates
Dammallam ya ƙara da cewa tun bayan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Gwamna Radda ya rage yawan motocin da ke raka shi zuwa Daura domin rage yawan kuɗin tafiya, kasancewar yana yawan ziyartar garin don dalilai na musamman.
“Yawanci tafiyar tana da motocin kusan uku ne kawai domin kauce wa yin tarin jerin gwanon mota kamar da,” in ji shi.
Sanarwar ta kuma karyata rade-radin da ke yaduwa a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa gwamnan na cikin wani hali mai tsanani.
BBC HAUSA