Manoma a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano sun nuna farin cikinsu tare da yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa raba taki na zamani a farashi mai rahusa ga manoman jihar a dukkan kananan hukumomi 44.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin ne a watan da ya gabata, da nufin karfafa samar da abinci da kuma inganta rayuwar manoma a lokacin daminar noma ta shekarar 2025.
An bijiro da Shirin ne domin taimaka wa kananan manoma da nufin bunkasa harkar noma musamman a matakin ƙasa.
A yayin da yake bayyana ra’ayinsa, Malam Mati Haladu daga gundumar Mai Nika ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa wannan tallafi.
Ya ce wannan shi ne karon farko da yake samun irin wannan taimako daga kowace gwamnati.
“Ina mika godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan taimako. Mun samu takin a kan lokaci kuma a farashi mai sauki. Wannan abin alfahari ne,” in ji Malam Haladu.
Ya kuma nuna godiya ga shugabancin karamar hukumar Gwarzo karkashin Dr. Mani Tsoho, bisa yadda suka tabbatar da isar da kayan tallafin ga manoma yadda ya dace.
Haka zalika, Malam Usman Abdullahi Tela daga gundumar Madadi ya bayyana jin daɗinsa kan wannan tallafi, inda ya bayyana cewa za su yi amfani da takin yadda ya dace, tare da bada tabbacin cewa ba za su sayar da shi ba, kamar yadda gwamnatin ta gargadi manoma.
A baya-bayan nan, Shugaban karamar hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho, ya jagoranci kaddamar da kwamitin rabon taki, a ofishinsa.
Ya umurci mambobin kwamitin da su gudanar da rabon cikin gaskiya da adalci domin tabbatar da cewa takin ya isa hannun manoman da aka nufa da shi.
Wannan mataki ana kallonsa a matsayin wata babbar gudummawa wajen farfado da harkar noma da kuma tabbatar da isasshen abinci a jihar Kano.