Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, ya yaba wa Kungiyar Shugabannin Kwalejojin Shari’a da Addinin Musulunci a Najeriya (COPCLIS) bisa jajircewarsu wajen ƙarfafa ilimin addinin Musulunci da na shari’a a fadin ƙasa.
Dr. Makoda ya yi wannan yabo ne a ranar Litinin yayin taron Zauren Tattaunawa na 48 na COPCLIS, wanda aka gudanar a Kwalejin Addini da Shari’a ta Aminu Kano, Kano.
Gwamnatin Imo ta Haramta bikin yaye Daliban Nursery da JSS 3
Kwamishinan Wanda Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Kididdiga na Ma’aikatar, Malam Yusha’u Hamza ya wakilta ya jaddada muhimmancin rawar da COPCLIS ke takawa wajen gina cibiyoyin ilimi da ke daga matsayin ilimi a Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
“Taron nan ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa ilimin addinin Musulunci da shari’a tare da gina al’adar ladabi, ilimi da kuma gina ƙasa. Ƙoƙarinku na inganta harkar ilimi ba shi da misaltuwa,” in ji Makoda.
Yayin da yake karɓar lambar yabo da aka ba shi, Dr. Makoda ya danganta wannan girmamawa ga haɗin kan Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
“Ina mika godiya ga COPCLIS da kuma shugabancin Kwalejin Addini da Shari’a ta Aminu Kano bisa wannan girmamawa. Wannan yabo ba nawa kawai ba ne, na dukkan tawagar Ma’aikatar Ilimi ce da ke aiki tukuru ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen inganta harkar ilimi a jiharmu. Allah Ya yi mana jagora wajen yada sahihin ilimi, ingantaccen ɗabi’a da kuma cigaban ƙasa,” in ji shi.
Gwamnan Kano ya Bada Umarnin Farfaɗo da Makarantar Faransanci da Sinanci
Dr. Makoda ya ƙara da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da yin haɗin gwiwa da COPCLIS da sauran abokan hulɗa wajen haɓaka ilimin addini, na shari’a da kuma ilimi gaba ɗaya domin dorewar ci gaba.
Sauran wadanda aka karrama a taron sun haɗa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo, da Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata.
Wannan girmamawa, a cewarsa, na nuna irin ƙudirin gwamnatin jihar wajen yin garambawul a harkar ilimi tare da neman haɗin gwiwar ƙwararru domin ƙarfafa bangaren ilimi.