A ƙoƙarinsa na bunƙasa ɓangaren ilimi da inganta koyo da koyarwa a jihar Kano, Gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin a gaggauta gyara makarantar koyon harsunan Faransanci da Sinanci mallakin gwamnatin jihar.
Wannan umarni dai ya fito ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar Kano, KwamaretComrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar bayan wata ziyarar bazata da gwamnan ya kai makarantar da ke garin Kwankwaso, a ƙaramar hukumar Madobi.
Read also: Speak Up Africa Partners Launch Private Sector Drive to End Malaria
A lokacin ziyarar, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa ya kai ziyara makarantar ne domin ya ganewa idonsa yadda ɗalibai da malamai ke gudanar da harkokinsu, da kuma yanayin gine-ginen makarantar.
Read also: Two Freed, Two Still Missing After Bandit Attack in Kano Community
Gwamnan ya bayyana jin daɗinsa bisa ƙwazon malamai da ɗaliban, musamman yadda ɗaliban ke iya magana da kyau da harsunan Faransanci da Sinanci.
Read also: NEMA Empowers NYSC EMVs with Disaster Management Skills
“Za mu gyara makarantar ba tare da ɓata lokaci ba,” in ji gwamnan, inda ya umarci Kwamishinan Ayyuka da ya hanzarta fara aikin gyare-gyaren gine-ginen da suka lalace a makarantar.
Wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin Kano na inganta ilimi da samar da ingantacciyar nagarta a fannin koyon harsuna domin bunƙasa ci gaban jihar.

