Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa wasu masu amfani da wutar lantarki a Nijeriya sun roƙe shi da a rage yawan wutar da ake samar musu, sakamakon ingantuwar samar da wutar lantarki a ƙasar.
Ministan ya ce wasu daga cikin masu amfani da wutar sun bayyana cewa yawan wutar da suke samu ya sa “firijinsu na daskarewa sosai”.
Read also: Da Dumi Dumi: Mahaifiyar Tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ta rasu
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Tegbe ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da aikin samar da hasken lantarki mai amfani da hasken rana, mai ƙarfin megawatt uku, a Jami’ar Abuja.
Read also: Academic Excellence: BUK Promotes Couple to Professional Rank
Ya ce al’ummar Nijeriya na ci gaba da cin gajiyar sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa a fannin wutar lantarki.
Tegbe ya bayyana ci gaban da aka samu a fannin a matsayin wani mataki da ke nuna cewa gyare-gyaren da ake yi a ɓangaren samarwa da rarraba wutar lantarki na fara haifar da sakamako.
Read also: PAACA Organizes Town Hall meeting on Electoral Reform
Ya ƙara da cewa ƙarin samar da wutar lantarki zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci, ilimi da sauran ayyukan ci gaba a ƙasar.
Daily Trust

