Wani jirgin sama da ke tafiya daga Dubai zuwa Tel Aviv, ɗauke da kimanin fasinjoji 170, ya yi saukar gaggawa a Saudiyya bayan da aka ruwaito cewa faɗa ya ɓarke tsakanin matuƙan jirgin.
Wasu jami’an Isra’ila biyu sun ce ana kyautata zaton mataimakin matuƙin jirgin ya daba wa babban matuƙin wuƙa.
Read also: FCT Begins Major Renovation of General Hospitals
Yayin da ƙarin bayanai ke fitowa daga fasinjojin jirgin, lamarin na ƙara zama mai ban mamaki da firgitarwa.
Jirgin ya aika da saƙon gaggawa cewa ana ƙoƙarin ƙwace shi. Sai dai bayanan da ke fitowa yanzu na nuna cewa ana zargin ɗaya daga cikin matuƙan jirgin ne da yunkurin ƙwace shi, ba wani fasinja ba.
Fasinjojin da ke cikin jirgin sun bayyana cewa jirgin ya fara gangarowa da sauri, inda ya sauka da kimanin ƙafa dubu 17 cikin ƴan mintuna.
An ce rikici ya ɓarke tsakanin matuƙin jirgin da mataimakinsa, inda aka daba wa aƙalla ɗaya daga cikinsu wuƙa.
Wani fasinja ya ce daga bisani wasu mutane suka kutsa cikin ɗakin matuƙan jirgin domin taimakawa wajen shawo kan ɗaya daga cikinsu, kafin su ɗaure shi.
Hotunan bidiyo da aka ɗauka da wayar salula sun nuna mutane da dama a cikin jirgin jikinsu na ɗauke da jini.
Read also: Kebbi Government Hails Army’s New Security Deployments
Yanzu masu bincike za su tantance ko ɗaya daga cikin matuƙan jirgin ya yi niyyar kifar da shi da gangan, da kuma ko akwai wata manufa ta siyasa a bayan lamarin.
Jirgin na ɗauke da kusan Isra’ilawa 100.
Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra’ila, Itamar Ben Gvir, ya bayyana lamarin a matsayin harin ta’addanci, yana mai cewa manufar ita ce kashe dukkan mutanen da ke cikin jirgin.
Wani bidiyo da kafofin yaɗa labaran Isra’ila suka wallafa ya nuna wani da aka ce yana cikin jirgin yana bayyana cewa wani mutum ɗauke da wuƙa ya daba wa ɗaya daga cikin matuƙan jirgin.
BBC Verify ta binciki bidiyon, kuma ba ta gano wata alamar cewa an sarrafa shi da fasahar AI ba.
Haka kuma, ba a ga alamar cewa an wallafa bidiyon a intanet kafin faruwar lamarin ba.
Isra’ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun ƙulla hulɗar diflomasiyya a shekarar 2020 ƙarƙashin yarjejeniyar Abraham Accords da Amurka ta shiga tsakani.
Read also: ACSITE Advocates Formal Education, Support for Islamic Schools
Yarjejeniyar ta daidaita hulɗar ƙasashen biyu. Kafin wannan yarjejeniya, an hana jiragen Isra’ila bi ta sararin samaniyar Saudiyya.
BBC HAUSA

