Hukumar kare haƙƙin masu saye ta Jihar Kano (KCPC) ta rufe wani shagon maganin gargajiya mai suna Kashiful Aleel, da ke kan titin Zoo Road a Kano.
Bayanin haka na ɗauke ne cikin sanarwar da Jamilu Mustapha Yakasai, jami’in hukumar ya fitar kuma aka wallafa a shafin Facebook na hukumar.
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano Ta Gayyaci Tijjani Gandu
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne biyo bayan wani ƙorafi da wani ɗan ƙasa ya shigar.
Read also: Kano Gov Hails Saudi Arabia for 52 Free Urological Surgeries
A halin yanzu, jami’an KCPC na gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin da ya jawo ƙorafin.
Read also: Kano Govt Pledges Support for NIPR, WPRF 2026
Hukumar ta kuma ce za ta sanar da jama’a sakamakon binciken da halin da ake ciki da zarar an kammala binciken.
Daily Nigerian Hausa

