An shiga cikin fargaba a birnin Sakkwato ranar Juma’a bayan da wani matashi ya daɓa wa wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukwa, jim kaɗan bayan ya jagoranci sallar Juma’a a masallacinsa da ke unguwar Mabera a birnin Sokoto.
Rahotanni sun ce matashin na cikin masu ibadar da suka halarci sallar, inda ake zargin ya caka masa wuƙa sau biyu a wuya, lamarin da ya nan da nan aka garzaya da shi asibiti.
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano Ta Gayyaci Tijjani Gandu
Read also: Kebbi Accord Candidate Pledges N500,000 Minimum Wage
Wani bidiyo da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook, jim kaɗan bayan sallamarsa daga asibitin ya nuna wuyansa ɗaure da bandeji, inda yake kiran magoya bayansa su kwantar da hankali.
Read also: Kaoje Attacks: Kebbi Gov Approves N200m Support
”Jama’a kowa ya kwantar da hankalisa, ina cikin ƙoshin lafiya, babu wata matsala, lafiyar ƙalau nake ban jin komai ga jikina, Allah ya bani kariya”, kamar yadda ya bayyana a cikin bidiyon mai tsawo sakan 32.
BBC HAUSA

