An kama wani boka a jihar Anambra bayan da ya amsa cewa yana karɓar kwaroron roba da aka yi amfani da su daga wajen ‘yan mata masu zaman kansu domin shirya tsafi.
Wanda ake zargin, mai suna Anagbo Emeka daga garin Umugbo a karamar hukumar Ayamelum, matasan ne suka kama shi a unguwar Echara, Awka North.
An Cafke Ma’aikaciyar jinya ta bogi bayan ta Kula da Marasa lafiya 4,400
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na Dr. Uche Nworah ya nuna lokacin da Emeka ya amsa laifinsa a fili.
Ya ce: “Na yi yarjejeniya da ita ta sayar min da kwaroron roba da aka yi amfani da su. Ta kawo min, amma daga baya ta kai rahotona. Wannan shi ne kuskuren da na yi,” in ji shi a cikin bidiyon.
A cewarsa, ya kulla yarjejeniya da wata karuwa da ta rika kawo masa kwaroron roba daga gidajen karuwai. Amma daga baya ta fasa alkawarin, ta tona asirin sirrin da suka ɓoye.
Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano ta Dakatar Da Fina-finai Guda 22
Emeka ya kuma bayyana cewa waɗannan kwaroron roba na da matuƙar amfani wajen harkokin tsafi da yake yi.
Ya ce: “Ina amfani da kwaroron roba wajen yin tsafi don sihiri, husuma, rikicin filaye, har ma da shari’ar ‘yansanda.”
Daily Nigerian Hausa

