Aisha Ahmed
A ranar Lahadin da ta gabata, abin ya fara kamar ziyarar nuna goyon baya da ɗan majalisar tarayya mai Wakilcin Birniwa, Guri da Kirikasamma yayi zuwa taron Gwamnati da Jama’a, da gwamnatin jihar Jigawa ke gabatarwa duk sati a kananan hukumomi 27 na Jigawa.
Amma abun ya rikide zuwa wani darasi da ba a yi tsammani ba, ganin yadda matasa suka bayyana ra’ayoyi masu tsauri irin na siyasa a zamanance.
Matasa a yankin sun bayyana fushinsu ta hanyar jefa maganganu na zamani da aka fi sani da slang na Gen Z.
Ɗan majalisar tarayyar, Dr. Abubakar Hassan Fulata, ya tarar da tatasa da dama da suka hallara domin nuna ɓacin ran su kan abin da suka bayyana a matsayin “shekaru na sakaci da rashin kulawa daga wakilinsu.”
Yanayi ya ɗauki zafi ne lokacin da ɗan majalisar ya yi ƙoƙarin yin jawabi, sai matasan suka katse shi da ihu da bakaken maganganu irin na Gen Z suna cewa bama yi, bama yi, karya ne karya ne, mai alkawarin bogi da sauran kalamai barkatai.
Wasu kuma sun ɗauki fastoci masu rubuce-rubuce kamar “Bama ganinka sai ka zo taron siyasa, wasu ma da turanci suka rubuta “No vibes, no votes.”
Kamar yadda suka zanta da manema labaru, wasu cikin matasan sun zargi ɗan majalisar da, mayar da hankali kan tarukan siyasa, yayin da yake watsi da matsalolin ci gaban zamantakewa da ke shafar matasan yankin har ma danginsa na jini.
Wani matashi manomin albasa mai suna Muhammed Umar ya shaida wa ‘yan jarida cewa, Fulata ba ya ziyartar al’umma ko da lokacin makoki, alhini ko wani abin damuwa a cikin iyalansa.
Haka kuma, Ibrahim Adam wani matashi a yankin Turabu, ya ce zuwan ɗan majalisar tare da ‘yan banga da masu bindiga a ranar taron, alama ce ta rashin gaskiya da amanar jama’ar da yake wakilta.
“Ina tambaya, idan ya amince da kansa da al’ummar da suka zabe shi, me ya sa zai zo mana da masu bindiga da mafarauta suna zagaye da shi kamar ya zo yaƙi da mu?” in ji Adam cikin ɓacin rai.
Jami’an tsaro da dattawan yankin sun yi iya ƙoƙarinsu domin hana tashin hankali da kuma mayar da hankali kan ainihin manufar taron.
Yayin da wasu mazauna yankin suka soki dabiar matasan saboda rashin ladabi, wasu kuwa sun kalli hakan ne a matsayin sabon salo na siyasa, inda matasa ke amfani da barkwanci, maganganun zamani wajen neman hakkinsu akan gaskiya da tsarin shugabanci nagartacce.
Wata ‘yar jam’iyyar APC a yankin, Hajiya Maryam Abubakar, ta ce, “Gen Z suna magana da sabon harshen siyasa a jihar Jigawa, kuma suna amfani da “slang” da al’adunsu na intanet.
Ko da yake tsoffin ‘yan siyasa na ganin hakan wasa ne, amma yana nuna zurfin ɓacin rai da gajiyawa daga salon da wasu ke tafiyar da mulki.
Labarin taron, wanda ya bazu a kafafen sada zumunta, ya sake tayar da muhawara kan yadda babu haɗin kai tsakanin ‘yan siyasa da matasa.
Mutane da dama a shafukan intanet sun yaba da abin da matasan Kirikasamma suka yi, suna cewa “sun faɗi gaskiya ga masu mulki” cikin salon da ya dace da zamani.
Wani ɗan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Jigawa, Malam Abubakar Wakili, ya ce abin da ya faru ya nuna sabon kalubale ga ‘yan siyasa a Najeriya.
“Muna ganin fitowar sabon salo na bayyanar matasa masu haɗin kai ta intanet, masu faɗin albarkacin bakinsu, waɗanda ke auna shugabanci a wani ma’auni na zahiri,” in ji shi.
Yayin da ihu da maganganun matasan Kirikasamma suka gushe daga tituna kuma ƙura ta lafa, saƙo guda ya rage a bayyane, Matasa Gen Z na Najeriya ba kawai a intanet suke ba, suna nan a fili, suna sauya tunani akan yadda taken dimokuraɗiyyar ƙasar zai kasance.
Irin wannan al’amari da ya faru a Kirikasamma, ya faru a kananan hukumomin Babura, Birnin Kudu, Gwaram da Gagarawa inda matasa suka hana ‘yan siyasa (da basa shugabanci na gari) katabus a lokaci taron Gwamnati da jama’a a yankunan.

