Close Menu
PARADIGM NEWS
    Facebook X (Twitter) Instagram
    • Home
    • Privacy Policy
    Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
    PARADIGM NEWS
    • Home
    • Features

      5 Key Facts About May Agbamuche-Mbu, Nigeria’s New INEC Boss

      October 8, 2025

      Happy Breadwinner A Story by Fatima Zahra Umar

      September 22, 2025

      Broken Rules, Unbroken Hearts Chapter One by Sadiya Datti

      September 21, 2025

      Abuja Marriage By Fatima Zahra Umar

      September 19, 2025

      How Women Farmers in Adamawa Are Leading Nigeria’s CSA Revolution

      September 5, 2025
    • News
      1. Local
      2. National
      3. International
      4. View All

      Kano Community in Shock as Missing Nonagenarian Found Dead in Toilet Pit

      November 7, 2025

      Water Tank Explosion Injures Several in Jigawa’s Malam Madori

      October 5, 2025

      Kano Govt Approves Construction of Two Major Roads in Gwarzo

      October 4, 2025

      Grief in Jigawa as 15-Year-Old Boy Drowns in Community Pond

      October 2, 2025

      FG Declares Open Technical Session of 47th NCAFS

      November 8, 2025

      UNESCO Names Nigeria Host of World’s First MIL Institute

      November 8, 2025

      WPRF-Abuja 2026; Etsu Nupe Becomes Royal Ambassador

      November 5, 2025

      NIPR President Urges Youths to Speak Positive of Nigeria

      November 5, 2025

      The Dakar Declaration on Health Sovereignty in Africa

      November 8, 2025

      Media Key to Health Sovereignty in Africa, REMAPSEN Tells Leaders at Galien Africa Forum 2025

      October 31, 2025

      Women Take Center Stage at Galien Africa Forum 2025

      October 30, 2025

      Young African Innovators Champion Health Sovereignty at 2025 Galien Africa

      October 30, 2025

      Kano Assembly Committee Inspects Ongoing Projects in Tarauni

      November 8, 2025

      Jigawa SAP III Targets Faster Justice for GBV Survivors -OGP Co-Chair

      November 8, 2025

      KNHA Moves to Certify Traditional Birth Attendants, Establish Medical Laboratory Directorate

      November 5, 2025

      FCCPC Seals Kano Outlets Over Sale of Under-Measured Fabrics

      November 5, 2025
    • Politics

      Former Kano Gov Shekarau Turns 70, Declares Lifelong Political Mission

      November 5, 2025

      PDP Re-elects Bello Suru as Chairman in Kebbi State

      September 30, 2025

      Online Reports False, I’ve Not Joined Any Party-Kwankwaso

      September 26, 2025

      Nigerians Ready to Re-Elect Tinubu in 2027– Jigawa Governor

      September 25, 2025

      APC Chair Lauds NPC DG’s Efforts to Strengthen Youth Dev in Kano

      September 16, 2025
    • Conflict

      Natasha Livestreams Faceoff With Immigration Over Passport Seizure

      November 4, 2025

      Kebbi Gov’t Threatens Legal Action Against Malami Over Defamation Claims

      September 19, 2025

      FG Calls for Conflict-Sensitive Climate Adaptation to Tackle Insecurity

      September 3, 2025

      Kadpoly Retiree faults Committee, Demolition Of Property

      March 27, 2025

      President Tinubu Declares State of Emergency in Rivers State

      March 18, 2025
    • More
      • Analysis
      • Business
      • Crime
      • Cultural events
      • Economy
      • Education
      • Editorial
      • Entertainment
      • Environment
      • Fashion
      • Health
      • Lifestyle
      • Personality profile
      • Science
      • Sports
      • Technology
    • Hausa

      Allah Sarki! Ma’aikatan Wucin-gadi na Kafafen Yada Labarai

      November 6, 2025

      An Cafke Mutumin da yayi Garkuwa da ‘yayan dan’uwan sa a Bauchi

      October 27, 2025

      Rikici Ya Sa KNSG Rushe Hukumar Kare Masu Amfani da Kaya

      October 25, 2025

      Hisbah Ta Sanya Maiwushirya da ‘Yar Guda Cikin Auren Gata na Kano

      October 21, 2025

      Yadda sabon yaren Gen Z ya fara horar da ‘Yan Siyasa a Jigawa

      October 14, 2025
    Subscribe
    PARADIGM NEWS
    Home » Yadda sabon yaren Gen Z ya fara horar da ‘Yan Siyasa a Jigawa
    Hausa

    Yadda sabon yaren Gen Z ya fara horar da ‘Yan Siyasa a Jigawa

    EditorBy EditorOctober 14, 2025Updated:October 14, 2025No Comments4 Mins Read
    Facebook Twitter Telegram WhatsApp
    IMG 20251014 WA0191

    Aisha Ahmed

    A ranar Lahadin da ta gabata, abin ya fara kamar ziyarar nuna goyon baya da ɗan majalisar tarayya mai Wakilcin Birniwa, Guri da Kirikasamma yayi zuwa taron Gwamnati da Jama’a, da gwamnatin jihar Jigawa ke gabatarwa duk sati a kananan hukumomi 27 na Jigawa.

    Amma abun ya rikide zuwa wani darasi da ba a yi tsammani ba, ganin yadda matasa suka bayyana ra’ayoyi masu tsauri irin na siyasa a zamanance.

    Ad 4

    Matasa a yankin sun bayyana fushinsu ta hanyar jefa maganganu na zamani da aka fi sani da slang na Gen Z.

    Ɗan majalisar tarayyar, Dr. Abubakar Hassan Fulata, ya tarar da tatasa da dama da suka hallara domin nuna ɓacin ran su kan abin da suka bayyana a matsayin “shekaru na sakaci da rashin kulawa daga wakilinsu.”

    Yanayi ya ɗauki zafi ne lokacin da ɗan majalisar ya yi ƙoƙarin yin jawabi, sai matasan suka katse shi da ihu da bakaken maganganu irin na Gen Z suna cewa bama yi, bama yi, karya ne karya ne, mai alkawarin bogi da sauran kalamai barkatai.

    Isa Kaita College

    Wasu kuma sun ɗauki fastoci masu rubuce-rubuce kamar “Bama ganinka sai ka zo taron siyasa, wasu ma da turanci suka rubuta “No vibes, no votes.”

    Kamar yadda suka zanta da manema labaru, wasu cikin matasan sun zargi ɗan majalisar da, mayar da hankali kan tarukan siyasa, yayin da yake watsi da matsalolin ci gaban zamantakewa da ke shafar matasan yankin har ma danginsa na jini.

    Ash Noor

    Wani matashi manomin albasa mai suna Muhammed Umar ya shaida wa ‘yan jarida cewa, Fulata ba ya ziyartar al’umma ko da lokacin makoki, alhini ko wani abin damuwa a cikin iyalansa.

    Haka kuma, Ibrahim Adam wani matashi a yankin Turabu, ya ce zuwan ɗan majalisar tare da ‘yan banga da masu bindiga a ranar taron, alama ce ta rashin gaskiya da amanar jama’ar da yake wakilta.

    “Ina tambaya, idan ya amince da kansa da al’ummar da suka zabe shi, me ya sa zai zo mana da masu bindiga da mafarauta suna zagaye da shi kamar ya zo yaƙi da mu?” in ji Adam cikin ɓacin rai.

    Jami’an tsaro da dattawan yankin sun yi iya ƙoƙarinsu domin hana tashin hankali da kuma mayar da hankali kan ainihin manufar taron.

    Yayin da wasu mazauna yankin suka soki dabiar matasan saboda rashin ladabi, wasu kuwa sun kalli hakan ne a matsayin sabon salo na siyasa, inda matasa ke amfani da barkwanci, maganganun zamani wajen neman hakkinsu akan gaskiya da tsarin shugabanci nagartacce.

    Wata ‘yar jam’iyyar APC a yankin, Hajiya Maryam Abubakar, ta ce, “Gen Z suna magana da sabon harshen siyasa a jihar Jigawa, kuma suna amfani da “slang” da al’adunsu na intanet.

    Ko da yake tsoffin ‘yan siyasa na ganin hakan wasa ne, amma yana nuna zurfin ɓacin rai da gajiyawa daga salon da wasu ke tafiyar da mulki.

    Labarin taron, wanda ya bazu a kafafen sada zumunta, ya sake tayar da muhawara kan yadda babu haɗin kai tsakanin ‘yan siyasa da matasa.

    Mutane da dama a shafukan intanet sun yaba da abin da matasan Kirikasamma suka yi, suna cewa “sun faɗi gaskiya ga masu mulki” cikin salon da ya dace da zamani.

    Wani ɗan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Jigawa, Malam Abubakar Wakili, ya ce abin da ya faru ya nuna sabon kalubale ga ‘yan siyasa a Najeriya.

    “Muna ganin fitowar sabon salo na bayyanar matasa masu haɗin kai ta intanet, masu faɗin albarkacin bakinsu, waɗanda ke auna shugabanci a wani ma’auni na zahiri,” in ji shi.

    Yayin da ihu da maganganun matasan Kirikasamma suka gushe daga tituna kuma ƙura ta lafa, saƙo guda ya rage a bayyane, Matasa Gen Z na Najeriya ba kawai a intanet suke ba, suna nan a fili, suna sauya tunani akan yadda taken dimokuraɗiyyar ƙasar zai kasance.

    Irin wannan al’amari da ya faru a Kirikasamma, ya faru a kananan hukumomin Babura, Birnin Kudu, Gwaram da Gagarawa inda matasa suka hana ‘yan siyasa (da basa shugabanci na gari) katabus a lokaci taron Gwamnati da jama’a a yankunan.

    Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram WhatsApp

    Related Posts

    Allah Sarki! Ma’aikatan Wucin-gadi na Kafafen Yada Labarai

    November 6, 2025

    An Cafke Mutumin da yayi Garkuwa da ‘yayan dan’uwan sa a Bauchi

    October 27, 2025

    Rikici Ya Sa KNSG Rushe Hukumar Kare Masu Amfani da Kaya

    October 25, 2025

    Hisbah Ta Sanya Maiwushirya da ‘Yar Guda Cikin Auren Gata na Kano

    October 21, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Editors Picks

    Kano Assembly Committee Inspects Ongoing Projects in Tarauni

    November 8, 2025

    Kano, Partners Validate Tom Brown to Boost Local Nutrition

    November 8, 2025

    Jigawa SAP III Targets Faster Justice for GBV Survivors -OGP Co-Chair

    November 8, 2025

    NUGA 2025 : BUK VC Charges Athletes to Be Good Ambassadors

    November 8, 2025
    • Facebook
    • YouTube
    • TikTok
    • WhatsApp
    Hajaj Albait 2
    © 2025 PARADIGM NEWS
    • Home
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.