Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa jagoran Ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin bayyana tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar Kano.
A tuna cewa Abdussalam ya yi murabus daga mukaminsa na mataimakin gwamna a watan Maris, makonni kaɗan bayan Majalisar Dokokin Jihar Kano ta aika masa da takardar tsige shi daga mukamin.
Majiyoyi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa ta sirri da aka gudanar a tsakanin jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da abokan siyasa na kusa da Kwankwaso.
Tun da fari dai tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, na daga cikin waɗanda ake ganin su ne na gaba-gaba wajen samun tikitin takarar gwamnan.
Sai dai rahotanni sun ce daga ƙarshe Kwankwaso ya amince da Abdussalam a matsayin wanda zai baiwa takarar.
Rahotannin sun ƙara da cewa Kwankwaso ya yi wa Gawuna tayin kujerar mataimakin gwamna ko kuma tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, amma ana ganin Gawuna ya ƙi amincewa da tayin tare da jaddada biyayya da ci gaba da aiki domin nasarar jam’iyyar.
Majiyoyi sun ce Gawuna ya shaida wa Kwankwaso cewa ya shiga tafiyar Kwankwasiyya ne ba tare da wani sharadi ba, saboda haka rashin samun tikitin gwamna ba zai sa ya fice daga tafiyar ba.
An kuma rawaito cewa ƙin amincewar Gawuna da tayin ne ya jinkirta sanar da Aminu Abdussalam a hukumance, yayin da wasu masu ruwa da tsaki ke matsa lamba kan a sake duba cancantar Gawuna saboda ƙarfin siyasarsa.
Wasu daga cikin masu goyon bayan Gawuna sun bayyana cewa ya kamata ɗan takarar da zai fafata da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito daga Kano ta Tsakiya, kasancewar yankin ne ke da mafi yawan ƙuri’u a jihar.
Sai dai masu goyon bayan Aminu Abdussalam suna ganin tsohon mataimakin gwamnan ya nuna cikakkiyar biyayya, jajircewa da sadaukarwa wajen bunƙasa tafiyar Kwankwasiyya.
Daily Nigerian Hausa

