A wani wasan da ya ƙayatar kuma aka yi ta zura ƙwallo kamar ba gobe, a ƙarshe Ingila ta samu nasara kan Faransa da ci 6-4 wanda ya ba ta damar lashe lambar tagulla a Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Tun kafin a je hutun rabin lokaci ne Ingila ta zurara wa Faransa ƙwallo huɗu, amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Faransa ta dawo da ƙarfinta, sai dai lokaci ya ƙure.
Haka nan a wasan an kafa tarihi, inda baya ga Kylian Mbappe da ya zura ƙwallo biyu, 10 kenan a gasar bana, kuma mafi yawa da kowane ɗan wasa ya taɓa zurawa a tarihi (22), ɗan wasan Ingila kuma Bukayo Saka ya ci ƙwallo uku rigis.
Declan Rice ne ya fara jefa ƙwallo tun a minti na uku da fara wasa, sai Konsa ya zura ta biyu a minti na 18 bayan Rice ya ɗauko bugun ƙusurwa.
A minti na 37, Bukayo Saka wanda tauraruwarsa ta haska a wasan ya ci ƙwallo ta farko, sannan ya ƙara ta biyu a minti na 45+1, jim kaɗan kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Kylian Mbappe ya zura ƙwallo biyu a minti na 48 da na 66, Barcola ya zura a minti na 54.
Sai Bukayo Saka ya cike ƙwallonsa ta uku a bugun fenariti a minti na 87.
Amma a minti na 90+6, Ousman Dembele ya ci tasa ƙwallon guda ɗaya, inda shi kuma ɗanwasa Jude Bellingham ya shafa fatiha da wata ƙayatacciyar ƙwallo da ya zura a ragar Faransa a minti na 90+8, wanda hakan ya sa Bellingham ya ci ƙwallo 7 jimilla a gasar bana.
A karon farko a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, zakarun gasar za su samu wata kyauta ta musamman baya ga kofin da lambar yabo ta zinariya, za a bayar da zobe wato (championship ring).
Wannan sabon tsari ya samo asali ne daga al’adar wasannin Amurka, inda ake bai wa zakarun manyan gasa zobba na musamman domin tunawa da nasararsu.
Ƴan wasan da za su lashe wasan karshe tsakanin Argentina ko Sifaniya, za su karbi lambobin yabo na zinariya kamar yadda aka saba, sannan kuma za su samu wadannan zobba na tarihi.
Za a buga wasan karshe ne ranar Lahadi a filin wasa na MetLife da ke East Rutherford a New Jersey.
An riga an tsara zoben, inda a gefe guda za a ajiye Kofin Duniya, yayin da daya gefen za a sa zoben.
Bayan an tashi daga wasan karshe, kocin tawaga da kyaftinta za su karbi wani zobe na wucin gadi. Daga baya idan an kammala kera shi, za a maye gurbinsa da asalin zoben a hukumance. Sauran ƴan wasan kasar za su karbi nasu zobban a wani lokaci a gaba.
Jimillar zobba 2,026 ne kawai za a kera, kuma kowanne zai kasance da lambar sa ta musamman. Daga cikinsu, 30 za a bai wa tawagar da ta lashe gasar, yayin da sauran za a sayar wa jama’a. Har yanzu ba a bayyana farashin su ba.
Idan Argentina ta lashe gasar, za ta zama kasa ta farko da ta kare kambunta a jere tun bayan Brazil a shekarar 1962. Ita kuwa Sifaniya, tana neman lashe kofin duniya karo na biyu bayan nasararta ta farko a shekarar 2010.
A gefe guda kuma, Ingila da Faransa za su kara a ranar Asabar domin tantance wanda za ta kare gasar a matsayi na uku.
BBC HAUSA

