Kwamitin Musamman na Gwamnatin Jihar Kano kan Gine-ginen da ba a yi bisa ka’ida ba ya umarci a gaggauta cire wata katafariyar kofa da aka gina a kan hanyar jama’a a unguwar Rimin Auzinawa, Tudun Yola C, da ke Karamar Hukumar Ungogo.
Shugaban kwamitin, Dakta Dalhatu Aliyu Sani, ya bayar da umarnin ne yayin da ya kai ziyarar tantancewa yankin bayan korafe-korafen da mazauna suka gabatar kan lamarin.
Dakta Sani, wanda kuma shi ne Darakta Janar na Hukumar Tsara Taswirar Filaye ta Jihar Kano (KANGIS), ya ce binciken ya biyo bayan koken da al’ummar yankin suka rubuta, inda suka zargi Magaji Isyaka Mai Hula da tare hanyar jama’a ta hanyar gina katafariyar kofa.
Ya ce mazauna yankin sun bayyana cewa kofar ta hana su zirga-zirga cikin ‘yanci duk da roko da kuma umarnin da jami’an ‘yan sanda suka taba bayarwa na cire ta.
Shugaban kwamitin ya umarci Magaji Isyaka Mai Hula da ya cire kofar nan take, tare da gabatar da Takardar Mallakar Fili (Certificate of Occupancy) da sahihiyar takardar izinin gini a gaban kwamitin.
Ya jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da duk wani gini da ya saba wa dokokin tsara birane ko kuma ya hana jama’a amfani da hanyoyin da suke mallakar kowa ba.
Dakta Sani ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kuduri aniyar kare muradun al’umma da tabbatar da bin doka wajen gudanar da ayyukan gine-gine a fadin jihar.
Da yake magana a madadin mazauna yankin, Barista Aminu Garba Sabonsara ya yabawa gwamnatin jihar bisa yadda ta yi gaggawar daukar mataki kan koken da suka gabatar, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewar gwamnatin wajen kare hakkokin al’umma.

