Hukumar da ke Shirya Aikin Hajji ta Kasa a Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa an ja hankalinta kan wani rahoto da gidan jaridar THISDAY ya wallafa mai taken” 2027 HAJJ: Masu shirya Aikin Hajji Masu Zaman Kansu Sun Bukaci bayani kan Karkatar da Kujerun Aikin Hajji 5,000,” baya ga wasu labarai da ke zama na karya da wasu tsirarun masu lasisin shirya aikin Hajji suke yadawa a dangane da kujerun aikin Hajjin na 2027.
A cewar martanin ko sanarwar da Hukumar ta NAHCON ta fitar dauke da sa hannun Shafii Sani Mohammed babban jami’i mai kula da harkokin yada labarai da wallafa a hukumar ta NAHCON, yace duk da cewa masu ruwa da tsaki na bukatar ayi masu bayani kan abin da ya shafi harkokin aikin Hajji, yana da kyau a san muhimmanci na banbance gaskiya daga jita-jita dama lura da wasu abubuwan da ake yi bisa wata bukata ta kasuwanci.
Read also: Daura Emir Confers Traditional Title On Hajiya Baraka Sani
Sanarwar tace hukumar tana sane da yadda ake tsara wasu zarge-zarge marasa tushe kan batun na “Karkatar da Kujerun aikin Hajji” mai makon a bayyana wasu abubuwa da aka yi bisa kuskure, sai ake fitar da wasu zarge-zarge don kawar da hankali, daga batun gazawar masu shirya aikin Hajjin masu zaman kansu kan wasu sharuda masu tsauri da ake gindaya masu da wa’adi da ake basu da bin tsarin shigar da bayanai a tsarin fasahar zamani ta digital, sharudan da hukumar Aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta gindaya su saboda Hajjin da za a yi a 2027.
Abin lura shine yadda aka rubuta rahoton ba tare da bayyana wanda ke zargin hukumar ba sai kawai aka kira su da sunan “Masu ta cewa kan abin da ya shafi masu shirya tafiye-tafiye da ke zaman kansu,” Ba a fayyacewa masu karatu shin su waye wadannan masu shirya tafiye-tafiye, shin masu ruwa da tsaki ne ko kuwa wadanda suka gaza samun damar yin wannan aiki ne, ko wadanda suke gasa da takwarorinsu ko kuwa wadanda damar da aka basu bata dace da bukatarsu ba ta kasuwanci. Rashin bayyana kai ya sanya masu karatu sun gaza gano sahihancinsu da dalilin yin haka ko manufarsu.
Wani abun mai muhimmanci shine, duk da cewa wannan zargi abu ne da ke bukatar taka tsantsan, babu wata sheda da aka gabatar da ta nuna cewa ga wani abu da aka yi bisa kuskure.
Babu inda aka nuna ba da wadannan kujeru 5,000 an sabawa dokar kasar Saudiyya ko sharudan hukumar NAHCON ko duk wani tsari da ya shafi yadda ake gudanar da aikin Hajji a Najeriya. Bayanan dai sun fi kama da zato ko wata bukata ta kasuwanci, an gaza gabatar da hujja da ta nuna an karya doka ko wasu ka’idoji .
Tabbas, wannan rahoto ma ya nuna cewa hukumar ta NAHCON tayi bayani dalla-dalla kan yadda aka rarraba kujerun na aikin Hajji.Hukumar ta bayyana karara cewa kujerun da aka bawa Najeriya a Hajji 2027, su 50,000 ne,kuma kujeru 35,000 an ware domin jihohi da Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja sai kuma kujeru 15,000 da aka bawa masu jigilar aikin Hajji da ke zaman kansu da suke da lasisi.
Wadannan kujeru 15,000 an ware su ne ga masu shirya aikin hajjin da suke da lasisi kuma suke aiki karkashin kamfanoni (7) da aka aminta da su kamar yadda yake karkashin sharuda da aka gindaya a Najeriya da Kasa mai Tsarki ta Saudiyya.
NAHCON ta kara fayyace bayani da cewa kamafanoni da za su yi aikin Hajji da Umrah a 2027 kamfanoni ne da aka san da su wadanda ke da rijistar hukumar Corporate Affairs Commission (CAC) da wasu hukumomi na gwamnati da ke sanya idanu, kuma sai sun bi sharudan da ake gindayawa, kuma hukumar ta NAHCON ta basu lasisi cewa ta amince su gudanar da aikin Hajji da Umrah a 2027.
Duk da haka suna karkashin dokoki da tsari da ma iya fuskantar hukunci da ake iya yiwa duk mai gudanar da harkokinsa na jigila mai lasisi.
Sanarwar har ila yau ta kara da cewa ko da wasu masu ruwa da tsakin sun aminta da bayanan na NAHCON, wani abu ne na daban; a bangare guda idan za a yi adalci dole a fara duba matsayin hukumar bisa cancanta, ba wai a rufe idanu ba da zarge-zarge da bata suna.
“Magana ta gaskiya wanann cece-kucen ya fi kama da batu na kasuwanci, Harkokin aikin Hajji abune da ya shafi tattalin arziki inda za ka ga kamfanoni da dama suna fafutuka kan samun kujeru kayadaddu a tsakanin junansu.” A cewar sanarwar.
Ta kara da cewa batu ne kawai na na me masu kamfanonin za su samu ba ma batun ba da kariya ga mahajjata ba.
Read also: Data Sales Shift Online as Kano Vendors Battle Declining Patronage
Hukumar ta NAHCON ta kara da jan hankali na al’umma cewa “kalubalen da ke gaban masu shirya jigilar shine tsarin Saudi Nusuk-Masar da ke tafiya da lokaci a tsarin fasahar zamani na digital. Mahukunta a kasar Saudiyya sun bayyana karara cewa hanyar dora bayanan mahajjata da yi masu rijista za a rufe ranar 26 ga Satumba,2026.” Tace umarnin na ranar karshe daga hukumar ta kasar Saudiiya ne ba NAHCON ba, don ita bata hurumi na kara ko da minta daya ne.
A cewar sanarwar abin takaici maimakon mayar da hankali kan yin rijistar masu aniyar tafiya da sanya bayanan haihuwarsu da biyan kudade cikin lokacin da aka ka’idance, sai wasu daga cikin masu kamfanonin suka zabi bata lokacinsu wajen kirkirar labaran kanzon kurege da shirya labarai da za su boye matsalolin da suke da su wajen gudanar da ayyukansu.
Hukumar tace ba za ta lamunta ba tana gani kudaden da al’umma suka tattara wajen ganin sun sauke farali daga Najeriya a wofuntar da su saboda masu shirya jigilar sun gaza yin abin da ya dace na bin ka’idoji da Saudiyya ta gindaya. “Walwalar mahajjata muhimmiya ce dole duk masu jigila da ke da lasisi, ana bukatar ganin sun cika sharuda na yin abin da ake bukata cikin lokacin da Saudiyya ta ayyana”. A cewar hukumar.
NAHCON tace tana tattara bayanai na labaran karya da ake shiryawa da gangan don karkatar da hankali, a yaudari mahajjata da kokari sanya shakku ko karya gwiwa kan yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta na tsarin aikin Hajji.
“Duk masu shirya jigilar aikin Hajji da suka gaza sanya bayanan masu aniyar aikin Hajji wanda ke cikin sharadi na biyansu kudade kafin lokacin da Saudiyya za ta rufe damar da ta bayar, su za a kama da alhakin rashin cika sharudan.”
Hukumar ba za ta ji kunya ba wajen sanya takunkumi ciki kuwa har da dakatarwa ko janye lasisi ko sanya kamfanin cikin jerin masu laifi ko cikin bakin littafi idan bukatar hakan ta taso.
Hukumar ta NAHCON ta shawarci masu aniyar zuwa aikin Hajjin a bana da suka yi rijista da kamfanoni masu zaman kansu, su gaggauta bincikawa su tabbatar da ganin an shigar da bayanansu da yi masu rijista a tsarin na Nusuk kafin ranar 26 ga Satumba,2026 da ke zama cikar wa’adi.
Wani abun muhimmi kuma da ya kamata a fahimta irin wannan cece-kuce bai cika tsayawa a wallafa labari guda daya ba, kasancewar akwai bukata ta kasuwanci, ana iya samun rahotanni a kafafan yada labarai da gabatar da takardar tuhuma da nacewa wajen bibiya da matsi daga al’umma duk ana gabatar da su a kokari na ganin mahukunta sun janye matsaya da suka kafu akanta ko a tsaya kan a bin aka fi cin moriya. Irin wannan ba bakon abu ba ne a bangaren da ake fafutka da ta shafi tattalin arziki, sai dai duk da haka kafewa da kin karbar canji bai kamata a mayar da shi hujja ba ta yin wani abu na kuskure.
Takardar martanin hukumar ta NAHCON tace idan akwai wani abu da ake son a duba kan batun ba da kujerun Hajjin, ya kamata a gabatar da shi bisa hujja da bin ka’ida da hujjoji na hakika da bin hanyoyi na warware matsala ba kawai a rika gabatar da zargi ba kuma babu mai zargin, ko a rika kokari na bata suna.
‘Yan Najeriya na bukatar bayanai ne da aka samar bisa gaskiya da bin ka’ida da tantance hujja ba kawai a rika gina labarai ba kan zato da bacin rai ko zakuwa irin ta kasuwanci. Indai ba a ba da hujja ba komai na tsayawa ne a matakin na zargi kawai.
NAHCON tace tana nan daram wajen yin aiki da gaskiya da daidaito da bin diddigi da lura da walwalar mahajjata, Hukumar ba za a raba mata hankali ba, da wata fafutuka ta wadanda ba a sani ko suwaye ba, ba za ta kuma bari ba sakaci na wasu kamfanoni masu jigila kalilan ya shafi irin kimar da Najeriya take da ita ba a fagen shirya aikin Hajji a idanun duniya.
Read also: Kebbi Police Arrest 5 Suspects for Banditry, Reject ₦600,000 Bribe
A karshe hukumar ta aikin Hajji a Najeriyar NAHCON ta nunar da cewa duk abin da za a fadi a kafa hujja da gaskiya da bin ka’ida da Saudiyya ke shimfidawa da abubuwan da ke biyo baya na ka’ida ba wai a tsara bayanai ba wadanda babu masu su ko ya zamana a rasa manufar yinsu.
VON HAUSA

