Gwamnan Jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf, ya amince da hade Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi a matsayin wani muhimmin mataki na karfafa hadin kai wajen gudanarwa da kuma hanzarta gyare-gyare a bangaren ilimi na Jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi.
Bayan wannan sake fasalin, sabon tsarin zai ci gaba da aiki a karkashin sunan Ma’aikatar Ilimi, inda za a kafa wani sashe na musamman Ilimi Mai Zurfi a cikin ma’aikatar domin kula da harkokin manyan makarantu.
Sabon sashin zai kasance karkashin jagorancin Babban Sakatare (Permanent Secretary) tare da ma’aikatan da suka dace domin tabbatar da ingantaccen gudanar da manyan makarantu na jihar.
“Bisa wannan sabon tsarin, dukkan hukumomin da ke karkashin tsohuwar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi kamar Hukumar Ba da Tallafin Karatu (Scholarship Board) za su koma karkashin Ma’aikatar Ilimi, yayin da jami’o’in gwamnati na jihar da sauran cibiyoyin ilimi mai zurfi za su kasance karkashin kulawar sabon daraktan da aka kafa a cikin ma’aikatar da aka hade,” in ji sanarwar.
Wannan mataki na daga cikin ci gaba da gyaran da gwamnatin jihar ke yi a bangaren ilimi, wanda ke da nufin sake fasalta bangaren, kawar da maimaita ayyuka tsakanin hukumomi, inganta daidaita manufofi a dukkan matakan ilimi, tare da rage kudin gudanar da gwamnati.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wannan gyara an tsara shi ne domin rage kashe-kashen gwamnati tare da kara inganci, gaskiya da rikon amana, da kuma daukaka ingancin gudanar da harkokin ilimi a Jihar Kano.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa na da cikakken kuduri na aiwatar da manyan gyare-gyare da za su farfado da bangaren ilimi tare da tabbatar da kyakkyawar makoma ga matasa masu tasowa.
Saboda haka, an umarci Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jiha (Head of Service) da su tabbatar da aiwatar da wannan sauyi cikin gaggawa da kuma yadda ya dace tsakanin ma’aikatun da abin ya shafa da sassan su

