Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan alumma, Alhaji Mohammed Idris, ya ce manufofin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na bunƙasa masana’antu a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata suna ci gaba da samar da manyan ayyuka, ayyukan yi, ƙirƙire-ƙirƙire, da damarmakin tattalin arziki a faɗin ƙasar nan.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Talata a hedikwatar Hukumar Bunƙasa Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI) da ke Abuja, yayin rangadin da Tawagar Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa ta kai hukumar.
Ya ce an ƙaddamar da Rangadin Yaɗa Labarai na Ajandar Sabunta Fata ne domin bai wa ‘yan Nijeriya damar ganin ayyuka da shirye-shiryen da Gwamnatin Tarayya take aiwatarwa da idon su.
Ministan ya ce: “Muna son ‘yan Nijeriya su gani da idon su yadda manufofin gwamnati ke komawa ayyuka na zahiri, samar da ayyukan yi, ƙirƙire-ƙirƙire, da damarmaki. Ana ƙara tabbatar da gaskiya idan hukumomin gwamnati suna hulɗa kai-tsaye da jama’a, kuma ana ƙara ƙarfafa ɗaukar nauyi idan ‘yan ƙasa za su iya tantance cigaban da aka samu da kansu.”
Idris ya bayyana NASENI a matsayin muhimmiyar hukuma da ke jagorantar sauyin masana’antun Nijeriya ta hanyar kimiyya, aikin injiniya da fasaha, inda take aiwatar da ayyuka a fannonin masana’antun cikin gida, makamashi mai sabuntawa, aikin gona na zamani, fasahar zamani, da bunƙasa ƙwarewar ma’aikata.
A cewar sa, manufar Shugaba Tinubu ita ce gina tattalin arziki mai ɗorewa kuma mai dogaro da kai, wanda ya ta’allaƙa kan ƙirƙire-ƙirƙire, ƙara darajar kayayyakin cikin gida da kuma ƙarfafa gasa a fannin masana’antu.
Ya ce: “Manufar mu a bayyane take; ita ce sauya Nijeriya daga ƙasar da ta fi zama mai amfani da kayayyaki zuwa ƙasar da ke samarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.”
Ministan ya ƙara da cewa Ajandar Sabunta Fata ta sanya bunƙasa masana’antu, fasaha da ƙarfafa matasa a matsayin ginshiƙan sauya tattalin arzikin ƙasa, ta hanyar samar da yanayi mai kyau ga zuba jari, kasuwanci da samar da ayyukan yi masu ɗorewa.
Ya kuma yaba wa shugabanci da ma’aikatan NASENI bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa fasaha da hanyoyin aikin injiniya na cikin gida domin ƙarfafa ƙarfin samar da kayayyaki a ƙasar da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Haka kuma, Idris ya yaba wa membobin Tawagar Yaɗa Labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa bisa rawar da suke takawa wajen bayyana gaskiya ta hanyar yaɗa sahihan bayanai, rahotanni masu daidaito da kuma na gani da ido kan yadda ake aiwatar da manyan shirye-shirye da ayyukan gwamnati.
Tun da farko, Mataimakin Shugaban Hukumar kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NASENI, Khalil Suleiman Halilu, ya ce hukumar tana aiwatar da ingantacciyar dabarar bunƙasa masana’antu da ta mayar da hankali kan masana’antun cikin gida, musayar fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire a fannin kiwon lafiya da kuma amfani da binciken kimiyya wajen samar da kayayyaki.
Ya ce ayyukan NASENI yanzu sun shafi manyan sassa takwas na masana’antu, tare da aiwatar da ayyuka a dukkan shiyyoyin siyasar ƙasar nan guda shida da kuma Babban Birnin Tarayya.
Halilu ya ce: “Manufar mu ita ce gina masana’antu masu ɗorewa ta hanyar ƙera kayayyakin da suka dace da kasuwar Nijeriya, haɗa su a cikin gida, ƙara yawan abubuwan da ake samarwa a cikin gida a hankali, tare da gina masana’antun da za su iya yin gogayya a kasuwannin duniya. Ta haka ne muka samu damar kafa fiye da masana’antu 20 cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.”
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Cif Sunday Dare; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Daidaita Manufofi, Hadiza Bala Usman; Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Temitope Ajayi; Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Hulɗa da Jama’a da Shigar da ‘Yan Ƙasa Cikin Ayyukan Gwamnati; Malam Abdul’aziz Abdul’aziz; Mataimaki na Mussamman ga Shugaban Kasa kan Hudda da Jam’a da Wayar da Kai, da sauran manyan baƙi.
Daily Nigerian Hausa

