Tawagar masu shirya taron tuntuba na kwanaki biyu kan ci gaba da bunƙasa ƙananan yara a yankin Arewa maso Yamma, ta karrama Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, da lambar yabo ta jagoranci wajen ci gaban ƙananan yara.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Shugabar Shirin Bankin Duniya, Dokta Ritgak Tilley-Gyado, ta kai ziyarar godiya ga Sarkin Zazzau bisa halartar taron a matsayin Babban Bako.
An ba Mai Martaba Sarkin Zazzau lambar yabon ne bisa gudunmawarsa wajen wayar da kan al’umma da tallafawa shirye-shiryen da suka shafi jin daɗin yara, ilimi, lafiya da samar da abinci mai gina jiki a Masarautar Zazzau.
Da take jawabi, Dokta Tilley-Gyado ta yaba wa Sarkin Zazzau kan jagorancinsa da kuma yadda yake amfani da matsayinsa wajen tallata manufofin ci gaban ƙananan yara har zuwa yankunan karkara.
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Zazzau ya gode wa Bankin Duniya da Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya bisa wannan karramawa.
Sarkin ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da tallafawa duk wani shiri da zai tabbatar da cewa yara a Masarautar Zazzau sun samu lafiya, abinci mai gina jiki da ingantaccen ilimin farko.
Ya ce saka hannun jari a ci gaban ƙananan yara na da muhimmiyar rawa wajen gina al’umma mai ingantaccen makoma.
Bayan kammala ziyarar, Mai Martaba Sarkin Zazzau ya zagaya da tawagar wuraren tarihi da ke cikin harabar Fadar Zazzau, inda ya bayyana musu wasu muhimman wuraren tarihi na masarautar.
Taron na kwanaki biyu, wanda Bankin Duniya tare da Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya suka shirya, ya haɗa masu ruwa da tsaki daga jihohin Arewa maso Yamma domin tsara tsarin aiwatar da shirye-shiryen ci gaban ƙananan yara a yankin.
Taron ya kuma mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwa da tsara matakan da za su inganta ilimi, lafiya, abinci mai gina jiki da jin daɗin ƙananan yara a yankin Arewa maso Yamma.

