Maryam Danazimi Ibrahim, wata ‘yar takara daga Najeriya, ta lashe kyautar Naira miliyan 120, kwatankwacin Riyal dubu 300,000 na Saudiyya, bayan da ta zo ta farko a rukunin Tafsirin Mata na Izu 60, a gasar Alƙur’ani ta duniya ta 46 da aka kammala, wadda ake kira King Abdulaziz International Qur’an
Maryam, ƴar Jihar Gombe da ke Arewacin Najeriya, ta yi nasara a rukuni na biyu, wanda ya ƙunshi haddar Alƙur’ani gaba ɗaya tare da kyakkyawan karatu da bin ƙa’idojin Tajweed, da kuma Tafsir.
Maryam na daga cikin ƴan takara 50 — maza 25 da mata 25 — waɗanda aka bayyana a matsayin waɗanda su ka yi nasara a rukunnai biyar na gasar.
Ga yadda jadawalin waɗanda su ka samu nasara a rukuni na biyu ya ke:
Maryam Danazimi Ibrahim — Nigeria — SAR 300,000
Amat Al-Rahman Badi Mutahhar Kulaib — Bahrain — SAR 275,000
Amani bint Shaya bin Awad Al-Husaiki Al-Harthi — Saudi Arabia — SAR 250,000
Zainab bint Ibrahim bin Abdulsalam Idris — Saudi Arabia — SAR 235,000
Shumoukh bint Faiz bin Hamdan Al-Zanbaqi — Saudi Arabia — SAR 220,000
Ƙasar Saudiyya ta karrama waɗanda suka yi nasara a gasar King Abdulaziz International Competition ta 46, wadda aka gudanar domin haddar Alƙur’ani Mai Tsarki, karatunsa da tafsirinsa, da kyaututtukan da jimillar kuɗinsu ya kai Riyal miliyan 10.26.
Daily Nigerian Hausa

