Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya ce Nijeriya da Saudiyya suna zurfafa hulɗar su fiye da yadda take a baya, inda ake samun ƙarin haɗin gwiwa a fannonin noma, makamashi, zuba jari, sufurin jiragen sama, fasahar kuɗi (fintech) da kasuwanci.
Idris ya bayyana hakan ne, a wurin wata liyafar cika shekara 96 na Ranar Kasa ta Masarautar Saudiyya.
Read also: Peter Obi, IPOB and the Questions That Still Demand Answers
Ya ce: “A yau, hulɗar mu ta shiga wani sabon mataki na tattalin arziki da dabaru. Nijeriya da Saudiyya suna da damarmaki na zurfafa haɗin gwiwa a fannonin noma, makamashi, zuba jari, sufurin jiragen sama, fasahar kuɗi da kasuwanci.
“Waɗannan su ne fannonin da za su kawo amfani ga ƙasashen biyu tare da ƙarfafa hulɗar tattalin arzikin mu.”
Ministan ya ce an gina daɗaɗɗiyar hulɗar da ke tsakanin ƙasashen biyu ne bisa tarihi, addini, hulɗa tsakanin al’umma, da manyan buƙatu na bai-ɗaya, yana mai cewa ‘yan Nijeriya sun daɗe suna tafiya zuwa Saudiyya domin aikin hajji, karatu, kasuwanci da sauran dalilai.
Ya ce Nijeriya na iya koyi daga gogewar bunƙasar da Saudiyya ta samu, yayin da Gwamnatin Tarayya ke aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Gwamnatin na ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da nufin ƙarfafa tattalin arziki, inganta yanayin zuba jari, faɗaɗa ababen more rayuwa, da samar da ƙarin damarmaki ga ‘yan Najeriya,” inji Ministan.
Read also: Children’s Day: KNSG Reaffirms Commitment to Quality Education
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na zuba jari a tituna da hanyoyin jirgin ƙasa, tana inganta samar da wutar lantarki, tana kuma aiwatar da gyare-gyare a ɓangaren man fetur da iskar gas, tare da bai wa noma, masana’antu, fasahar dijital da tattalin arzikin ƙirkire-ƙirkire ƙarin kulawa.
Idris ya ce Nijeriya tana ƙoƙarin jawo ƙarin zuba jari na dogon lokaci ta hanyar samar da tsare-tsare bayyanannu ga masu zuba jari, yana mai cewa gyare-gyaren da aka yi kwanan nan a ɓangaren man fetur na teku an tsara su ne domin buɗe sababbin damarmakin zuba jari tare da ƙarfafa halartar ‘yan Najeriya.
“Muna maraba da masu zuba jari da ‘yan kasuwa daga Saudiyya da ke sha’awar Nijeriya. Akwai dama mai yawa ta haɗin gwiwa a fannonin noma da samar da abinci, makamashi, ababen more rayuwa, haƙar ma’adinai, fasaha da sauran fannonin samar da kayayyaki,” inji shi.
Ministan ya yaba wa Ofishin Jakadancin Saudiyya kan ƙoƙarin su na ƙarfafa huldar da ke tsakanin ƙasashen biyu, tare da bayyana ƙwarin gwiwa cewa hulɗar za ta ci gaba da ƙaruwa ta hanyar ƙarin kasuwanci, zuba jari, musayar ra’ayoyi da haɗin gwiwa.
Ya taya gwamnati da al’ummar Saudiyya murna kan bikin cika shekara 96 na Ranar Ƙasar su, yana mai fatan Masarautar ta ci gaba da samun zaman lafiya da wadata.
Read also: Trump to Withdraw U.S. from UNESCO Again, Slams “Woke”
Daga cikin manyan baƙi da suka halarci taron akwai Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Jakadan Masarautar Saudiyya a Nijeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi; Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu; tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, da wasu jami’an diflomasiyya da manyan ‘yan kasuwa.
DDL HAUSA

