A ‘yan kwanakin nan, an ga wasu ‘yan kwangila da aka dauka aiki, wadanda ba su san inda matsalar take ba, suna ta surutu da zarge-zarge marasa tushe balle makama. Su kansu ba su san inda suka dosa ba. Kuma ga dukkan alamu, hassada da haushi ne ke tafiyar da su domin su dakushe kima da darajar da Allah Ya yi wa Falgore.
To, ko sun so ko sun ki, fitilar Falgore ta haska kuma tana ci gaba da haskakawa a Karamar Hukumar Rogo da Jihar Kano baki daya.
Read also: FALGORE: THE PRIDE THAT SILENCES DETRACTORS
Idan kana son ganin shugaba nagari, jarumi, mai biyayya da cika alkawuransa ga al’ummarsa, to ka kalli Rt. Hon. Speaker Jibril Isma’il Falgore.
Falgore matashin dan siyasa ne, jagora mai karamci da hakuri, wanda zai ci gaba da dagula wa abokan hamayyarsa lamari. Domin kuwa, na gaba ya yi gaba, na baya sai labari. Haka kuma, hassada ga mai rabo taki ce.
A matsayinsa na Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, yana da dama da hakkin fadar albarkacin bakinsa a kan duk wani lamari. Kuma duk abin da yake fada, abubuwa ne da suka yi daidai da zahirin gaskiya. To, amma muna da tambaya: Shin ba gaskiya ba ne cewa ya yi musu alheri, su ma suka yi masa? Laifi ne yin hakan? Idan laifi ne, to sai a fada mana. Yana da kyau masu yada zantuka marasa tushe balle makama su fahimci yadda al’amura ke tafiya, duk da cewa jama’a na kallon su a matsayin shashashai.
Duk mutumin da ya yi mana kankara saboda Falgore, idan har ya ci gaba da yi masa katsalandan, to mu ma za mu mayar masa da martani mai karfi, irin na guduma mai sukkan dalma. Ko da yake, wadanda ke ta kunfar baki da surutai a kansa, tuni al’ummomin Rogo da Kano suka fara kallon su a matsayin wawaye da sakarkaru marasa daraja, kima, martaba da mutunci.
Haka kuma, ya kara tabbata cewa wadannan mutanen da ke ci gaba da yawo a tituna tare da yada maganganun banza a kafafen sada zumunta domin lalata tafiyar Mai Girma Speaker, mun gaya musu cewa sun makara, domin duk wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi.
Falgore gwarzo ne, haziki, masanin harkokin majalisa da dabarun mulki. A karkashin jagorancinsa, Majalisa ta samu gagarumin ci gaba. An samu nasarori da dama, ciki har da samar da dokoki wadanda daga bisani suka zama tubalin manufofin gwamnati, baya ga ayyukan raya kasa a yankunan Rogo da Karaye, gina sabon ginin Majalisar Dokokin Jihar Kano, da inganta albashi da walwalar ma’aikatan Majalisa. Wadannan nasarori sun janyo masa lambobin yabo da yabo daga sassa daban-daban na jihar.
Read also: Int’l Day of Rural Women: AECF Launches GALS to Empower Women in Kano
Falgore ya samu lambobin yabo a ciki da wajen Najeriya. A kwanakin baya ma, Kungiyar Ma’aikatan Majalisu ta Najeriya (PASAN) ta karrama shi a matsayin Speaker mafi tasiri a Najeriya, tare da amincewa da gudummawar da yake bayarwa wajen inganta walwala da yanayin aikin ma’aikatan majalisa.
Ko mun amince ko ba mu aminta ba, Falgore zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a siyasar Karamar Hukumar Rogo da Jihar Kano baki daya.
To, amma shawarar da muke bai wa wadancan ‘yan ciranin ita ce, akwai bukatar su fahimci cewa, duk da cewa watakila sun sani, amma kiyayya da hassada ne ke hana su amincewa da gaskiyar cewa rana ta fito, kuma tafin hannu ba zai iya kare ta ba.
Dukkanin ‘yan kwangilar da ke ci gaba da wannan soki-burutsu na banza, mutane ne da al’umma ke kara kallon su a matsayin wadanda ba su da alkibla, masu damfara da kage.
Shawarar da muke ba su ita ce su yi hankali, domin mutane na kallon su. Yarfen siyasa ba sabon abu ba ne, kuma ya kamata su yi nazari kan wadanda suka rika yin irin wannan abu a baya, su duba halin da suke ciki a yanzu. Don haka, ya rage nasu: ko dai su gyara halayensu ko kuma duniya ta koya musu hankali. Ya rage wa mai shiga rijiya ya yi abin da ya dace.
Falgore, kai gwarzo ne na kwarai. Ka ci gaba da gudanar da ayyukan alheri. Al’ummar Rogo na sane da kai, Jihar Kano na sane da kai, kuma mun yi imani cewa Allah, Wanda Ya halicce ka, yana sane da kai.
Gaba dai, gaba dai, Rt. Hon. Speaker Jibril Isma’il Falgore, jagoran Speakers na Najeriya.
Read also: 655,550 Households Reached Through CRoWN as Kano Takes MNCH to Communities
Rubutawa:
Kamaluddeen Sani Shawai
Mai magana da yawun Rt. Hon. Speaker
Kano State House of Assembly

