Malama ta maka FUD a kotu bisa kora da ɓata mata suna tare da neman diyya Naira Miliyan 120
Tsohuwar malama a Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD), Dr. Ramla Muhammad Kamal, ta kai ƙarar jami’ar da kuma magatakardan ta a Babbar Kotun Tarayya da ke Dutse, ta.na ƙalubalantar korar ta daga aiki tare da neman a biya ta Naira Miliyan 120 saboda zargin bata mata suna da kuma take haƙƙin ta na aiki.
Daily Trust ta rawaito cewa a cikin kundin ƙarar mai lamba FHC/DUT/CS/18/2026, Dr. Ramla, wadda ta kasance malama ce a mataki na biyu wato Lecturer II a Sashen Kimiyyar Magunguna (Pharmacology) na Tsangayar Kiwon Lafiya a jami’ar, ta ce korar da aka yi mata ba ta bi doka ba.
Ta yi zargin cewa jami’ar ta karya sharuddan aikin ta sabo da ba ta bata damar kare kan ta yadda ya kamata ba, sannan ta wallafa labarin korar tata da kuma bayyana ta a matsayin ma’aikaciyar da ta gudu daga aiki kafin ma ta karɓi wasiƙar korar.
Dr. Ramla na roƙon kotu ta ayyana wannan wallafa a matsayin bata suna, sannan ta umurci jami’ar ta janye wallafar, ta kuma ba ta hakuri a bainar jama’a, sannan ta biya ta Naira miliyan 100 a matsayin diyya ta gaba ɗaya da kuma Naira miliyan 20 a matsayin ƙarin diyya.
A cewarta, jami’ar ta ba ta izinin tafiya karatun digiri na gaba a Universiti Putra Malaysia tare da ci gaba da biyanta albashi, kuma ta kammala karatun a shekarar 2023.
Sai dai ta ce jami’ar ta ƙi amincewa da buƙatar, ta dakatar da albashinta daga Mayu 2024, ta fara binciken ladabtarwa, sannan daga bisani ta kore ta daga aiki a Yunin 2026 ba tare da ba ta cikakkiyar damar kare kanta ba.
Ta kuma yi zargin cewa labarin korarta da zargin cewa ta gudu daga aiki ya bazu a kafafen yaɗa labarai kafin ta karɓi wasiƙar korar, lamarin da ta ce ya bata mata suna.
A martanin ta, jami’ar da magatakardarta sun musanta dukkan zarge-zargen. Sun bayyana cewa aikin Dr. Ramla yana ƙarƙashin dokar Federal University Dutse Act, ƙa’idojin aiki na jami’ar da kuma yarjejeniyar hutun karatu da ta sanya wa hannu kafin tafiyarta.
Jami’ar ta ce ta cika dukkan alƙawurranta ta hanyar ci gaba da biyanta albashi da sauran haƙƙoƙin da aka amince da su, amma ba ta da wani nauyin biyan kuɗin makaranta, masauki, sufuri ko sauran kuɗaɗen karatunta.
Bangarorin biyu sun bayyana cewa za su gabatar wa kotu da takardu da suka haɗa da wasiƙun hutun karatu, yarjejeniyar hutun karatu, takardun binciken ladabtarwa, bayanan albashi, bayanan banki da sauran hujjoji.
Yanzu kotun ce za ta yanke hukunci kan ko wallafa sunan Dr. Ramla ya zama bata suna ko kuwa ba haka ba a zama na gaba.
Daily Nigerian Hausa

