Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da tallafin Sallah na naira dubu ashirin (N20,000) ga ma’aikatan gwamnati a fadin jihar da kuma kananan hukumomi 44.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Musa Tanko Muhammad, ya fitar a Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa an dauki matakin ne domin tallafawa ma’aikata gabanin bikin Babbar Sallah, bayan biyan albashin watan Mayun 2026 ga ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi.
Tallafin zai shafi ma’aikatan gwamnati masu mataki na 01 zuwa 14 da ke aiki a ma’aikatu, hukumomi da kananan hukumomi a fadin jihar.
Gwamna Yusuf ya ce wannan na daga cikin kudirin gwamnatinsa na kyautata jin dadin ma’aikata, wadanda ya bayyana a matsayin kashin bayan aikin gwamnati a Kano.
Ya kara da cewa an dauki matakin ne duba da halin matsin tattalin arziki da kuma bukatun bukukuwa, yana mai cewa tallafin zai taimaka wa ma’aikata gudanar da Sallah cikin walwala da kwanciyar hankali.
Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin inganta jin dadin ma’aikata, bunkasa aiki, da tabbatar da ingantaccen aikin gwamnati.
Haka kuma ya taya ma’aikatan gwamnati da al’ummar jihar Kano murnar Babbar Sallah tare da yi musu addu’ar zaman lafiya, hadin kai da ci gaba ga jihar da kasa baki daya.

