Harkokin karatu sun yi nisa a katafariyar cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote Mallakar Gwamnatin Jihar kano dake kan titin zuwa Zariya anan kano.
A wata ya ziyara izuwa makarantar an tarar dalibai 310 dake karatunsu a bana suna koyon sana’o’i daban daban a sassa Goma Sha Biyar.
A tattauna da shugaba mai Kula da harkokin gudanarwa na cibiyar Alhaji Alkasim Hussain Wudil ya ce tuni cibiyar ta kulla alaka da cibiyoyin kwararru akan ba da ilimin sana’o’i da kamfanoni domin tabbatar da nagartar ilimin da ake koyar musu tare da ba su damar kara sanin makamar aiki a kamfanoni da masana’antu dake ciki da wajen kasar nan.
READ MORE: Dangote varsity begins skill acquisition training
Wasu daga cikin daliban sun ce ko yanzu sun samun cikakken ilimin koyon sana’o’i wanda za su iya dogaro da kansu.
Daliban wadanda suka yi alkawarin mayar da hankali wajen karatunsu sun kuma bukaci gwamna Abba Kabir Yusuf da kananan hukumomi da suka dauki dukkanin nauyin karatun su samar musu da kayan cigaba da harkokin sana’o’insu idan sun kammala.
Daga cikin kwasa kwasan da daliban ke nazarinsu a aikace da kayan aiki na zamani sun hada da fannin gyaran motoci dana kera sassan mota da fannin gyaran AC dana Firji dan Dinki dana samar da Takalma da jakankuna na mata da maza da fannin Gini dana Samar da Hasken lantarki ta hanyar amfani da Rana ko Iska dana kera kayan daki da girkin biki da kwalliya da gyaran gashi da gyaran wutar lantarki dana Famfo da kuma na Kwamfuta da harkokin buga takardu da Zane Zane.
SIMILAR: Aliko Dangote Ultra Modern Skills And Acquisition Centre, Kano
Daliban na bana za su shafe watanni Hudu suna koyon karatu sannan za a tura su kamfanoni da masana’antu domin Kara kwarewa daga bisani a ba su shaidar kammala karatu mai daraja da za su iya amfani da ita a ciki da wajen kasar nan wajen samun aiki ko kuma su kafa na su masana’antun domin dogaro da kansu.
RK