Tubabbaun matasan da suka Ajiye makaman su a jihar Kano Sun bayar da tabbacin cewar zasu bayar da dukannin goyon bayan da ake bukata domin gudanar da zancen kananan hukumomin Lami lafiya.

Matasan Sun bayyana hakan ne yayin wata gamawa da Shugaban Kwamitin zaman lafiya na jihar Kano Ambasada Ibrahim Waiya ya shirya a Kano.

A jawabin sa tun da fari Shugaban Kwamitin na zaman lafiya yayi kira ga matasan da su gujewa bangar siyasa ta’addanci da Kuma duk wani abun da zai gurbata rayuwar su tare da haifar da koma baya ga zaman lafiyar alummar jihar Kano.

Ya ce gwamnatin jihar Kano a shirye ta ke wajen qaddamar da sabon shirin bunkasa rayuwar tubabbun da suka ajiye makaman su mai lakabin ‘ mu ma ‘yaya ne.

Ambasada Waiya ya bayyana takaicin sa a bisa yadda wadansu ‘yan siyasa ke gurbata rayuwar matasan ta habyar dora su a harkar shaye shaye dabar siyasa da sauran munanan ayyuka.

Shugaban kwamitin na zaman lafiya yayi tsokacin cewa duk wani Mai Neman ta da Zaune tsaye a yayin zaben na kananan hukumomi da ke tafe ba zai samu nasara ba duba ga irin nagartattun tsare tsaren da aka shirya.

Ya bayyana cewa jihar Kano ba zata taba gajiyawa ba wajen bunkara rayuwar tubabbaun matasan ta hanyar samar musu da ayyukan yi da sana’oin dogaro da Kai.

Ambasada Waiya yayi kira da tubabbun matasan da su cigaba da jajircewa wajen riko da nagartattun halaye domin inganta rayuwar su.

Ya basu shawarar baiwa sauran abokan su shararwarin su shigo cikin tsarin domin cimma nasarar da aka sa a gaba.

Wadansu daga cikin tubabbun matasan Star boy daga Kurna da sauran abokan sa Sun yi alkawarin cewa zasu bada dukannin goyon bayan da ake bukata domin yin Zane cikin lumana.

Sun yi kira ga Gwamnan jihr Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya cika musu dukannin alkawuran da ya dauka.

Suna Mai cewa Sun bar dukannin munanan halayen su tare da ajiye makamai Wanda Kuma basu da hanyoyin dogaro da Kai.

Idan zaku iya tunawa a ranar larabar da ta gabata ne shugaban kwamitin na zaman lafiya Ambasada Ibrahim Waiya ya shirya taron wayar da kan Alumma akan muhimmancin zancen na kananan hukumomi.

Idan yayi kira ga alummar jihar Kano dasu yi fitar dango wajen kada kuri’a domin sharbar romon demokradiyya

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version